Connect with us

MANYAN LABARAI

An Kai Hari Kan Tawagar Kamfen Din Jam’iyyar APC A Abuja

Published

on

Rikici ya barke a garin Dei-Dei da ke cikin babbar barnin tarayya wato Abuja, lokacin da wasu ‘yan daba suka kai wa tawagar yakin neman zaben jam’iyyar APC hari a ranar Asabar. Tawagar kamfen din jam’iyyar APC wanda ta kunshi wakilan ministan Abuja da shugaban jam’iyyar APC na garin Abuja Abdulmalik Usman da babban daraktan kamfen Musa Mohammed tare da ‘yan takara na mukamai da ban da ban na jam’iyyar da kuma dinbin magoya bayan jam’iyyar, an dai farmake su ne lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa fadar Sarkin Jiwa.
Mota guda tara ne daga cikin tawagar suka kone, yayin da wasu da dama aka fashe musu gilashi. Motane ‘yan kadan sun samu mummunar raunika. An dai farmakin jerin gwanon motocin jam’iyyar APC ne da tuwatsu, yayin da wadanda suka kone kuma an zuba musu fetur ne inda ka kunna musu wuta. Wasu kuma motocin an farfasa su. Ko da yake ba a samu asarar rayuka ba, jami’an tsaro sun ziyarci wajen da lamarin ya auku domin ka da rikicin ya watsu.
‘Yan daban sun tsare hanya ne a kusa da kasuwar Timber kan hanyar Dei-Dei, inda suka hana tawagar jam’iyyar APC zuwa fadar Sarkin Jiwa.
Wannan lamari dai ya faru ne lokacin da jam’iyyar PDP take gudanar da gangami a kasuwar Timber da ke Dei-Dei. Jami’an tsaro na ofishin minister da kuma sauran jami’an tson da ke tare da tawagar sun ta harbi sama domin su tarwatsa ‘yan daban da suka tsare hanya. An kara farmakin jarin gwanon motoci na karshe na kamfen din jam’iyyar APC, a wannan hanya lokacin da suke dawowa daga fadar a kusa da tsohon filin taro.
A farmaki na biyu ne aka kone mota tara da kuma sauran motocin da aka fashe musu gilashi. Jami’an tsaro sun yi gaggawar zuwa wajen da lamarin ya auku, inda suka tunga harbe-harbe a sama domin tarwatsa maharani. Jami’an tsaro sun taimaki tawagar kamfen jam’iyyar APC, inda suka buda musu hanya suka wuce. Wata mota duk da ba ta cikin tawagarm, amma said a ‘yan daban suka fasa mata gilashi. Zuwan jami’an tsaro ne ya kwantar da wannan rikici. Motocin da aka sakawa wuta suna ta ci tun daga rana har zuwa yamma.
Wadanda lamarin ya auku a gaban idanunsu sun bayyana cewa, ba a san wadanda suka shirya wannan farmakin na yakin neman zaben APC ba.
Babban daraktan kamfen din jam’iyyar APC na garin Abuja Musa Mohammed danganta wannan farmakin a matsayin abun bakin cikin. Ya kara da cewa, bayanin sirri sun huna cewa dama tun farko an shirya wannan farmaki ne. Duk da haka, Mohammed ya yi saurin daurawa ‘yan barandar jam’iyyar PDP, da kai alhakkikin wannan farmaki. A cewar Mohammed, “Bana dauka cewa wannan rikici ne a jam’iyya guda biyu. Mun san dai an kai wa tawagar jam’iyyar APC hari, amma ba mu san dalilin kai wannan farmaki ba.
“Wannan abin bakin cikin ne ya faru. Muna cikin tafiya aka farmake mu, haka ma sanda muke dawowa nan ma aka sake kai mana hari. “Amma muna jiran mu ga hukuncin da za a dauka, muna kokarin bin matakin da ba za a bi ba tare da an samu asarar rai ba. Ya ce, abin takaici ne a samu an kai irin wannan farmakin, an kone wasu motocin. “Bisa rahoton da na samu daga wajen jami’an tsaro, mota guda tara ne aka kona. Sauran motocin kuma da suka tsira an fasa musu gilashi. Mutane kadan kuma sun samu mummunar raunuka. “Mun tabbatar da cewa ana irin wannan ta’addancin kafin zabe. A kan haka ne na ke kira a samu gudanar da tsarin tsaro kafin zabe da kuma bayan zabe,” in ji Mohammed.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!