Connect with us

SIYASA

APC A Zamfara: Gamayyar ‘Yan Takara 8 Sun Fallasa Asirin Gwamna Yari

Published

on

Gamayyar ‘yan takarar gwamna takwas qarqashin inuwar jam’iyyar APC a Jihar Zamfara sun fallasa wani shiri na gwamna Abdul’aziz Yari na son yin amfani da qarfin gwamnati wurin shirya maqarqashiya da kotu don a tilastawa INEC wurin amsar ‘yan takarar APC tsagin gwamnan.

Gamayyar ‘yan takarar sun yi wannan tonon silili ne a wurin taron manema labarai da suka gudanar shekaran jiya Lahadi a Jihar Kaduna.

Sanata Kabir Garba Marafa wanda shi ne yayi jaawabi a madadin gamayyar ‘yan takarar, ya bayyana cewa, wannan shiri na gwamna Yari ba komi bane face yarinta da rashin sanin ciwon kai.

Tawagar gamayyar ‘yan takarar G8 din sune; Sanata Marafa, Dakta Dauda Lawal (Gamjin Gusau), Malam Ibrahim Wakala, Mahmuda Shinkafi, Mansur Dan-Ali, Aminu Sani Jaji, Abu Magaji, da kuma Mohammed Sagir Hamidu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!