Connect with us

WASANNI

Arsenal Na Son Siyan Dembele

Published

on

Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta fara zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Ouseman Dembele domin yakoma kungiyar a kakar wasa mai zuwa.
Dembele, mai shekara 20 yakoma Barcelona ne daga kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund a farkon kakar da ake bugawa bayan da kungiyar ta biya fam miliyan 97 domin siyan dan wasan, bayan sun siyar da Neymar zuwa kungiyar PSG dake kasar faransa.
Sai dai tun bayan komawar dan wasan Barcelona yake fama da rauni yayinda kuma a kwanakin baya yasamu rashin jituwa da kociyan kungiyar sakamakon rashin zuwa filin daukar horon akan lokaci wanda kuma kungiyar tace bazata amince ba.
Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Unai Emery, ya bayyana aniyarsa ta daukar dan wasan domin cigaba da gina kungiyar da sababbin ‘yan wasa inda a watan Janairu ya dauki aron dan wasa Denis Suares daga Barcelona
Kociyan kungiyar dai a kwanakin baya ya bayyana cewa kungiyar bazata iya siyan dan wasa ba sai dai ta karba aro a watan Janairun daya gabata saboda matsala ta kudi wadda tasa dole kungiyar tana bukatar siyar da wani dan wasan.
Kawo yanzu dai Arsenal tana mataki na biyar akan teburin na firimiya kuma har yanzu tana fafatawa a gasar cin kofin nahiyar turai wato europa sai dai tuni Manchester United tayi waje da ita a gasar cin kofin kalubale na FA.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: