Connect with us

ADABI

Asadul Muluuk (28)

Published

on

Da zuwansu aka sauko da ita daga kan taguwar, Ummu Nazifah ta ce; “Ranki ya dade wadannan jama’ar fa sun zo ne don su ga ‘yar Sarkinsu, wadda a duk shekara sau daya su ke ganinta.”
Gimbiya ta ce; “ Sun yi kyan kai, amma dai kin san ba don su muka zo ba ko?” yanzu ta yaya zan fahimci Asadulmuluuk ya zo wurin nan.? Ummu Nazeefah ta ce; “A yanzu dai babu hali har sai jama’a sun yi sauki, abin da zai fi kyau kawai shi ne, ki fito ki tsaya kamar dakika biyar, ki bude fuskarki, sannan ki daga musu hannu, hakan shi zai rage yawansu, sannan za ki samu kyakkyawan yabo daga gare su.”
Hakan kuwa aka yi, a lokacin da ta fito ta dagawa mutane hannu da nufin karbar gaisuwa, haba! jama’a ana sowa ana ta yi mata kirari tana karbar gaisuwa, suna ta murnar sun ga Gimbiyarsu, ita kuma tana tunanin yadda za ta ga masoyinta. Ummu Nazifa ta fahimci gimbiya fa kawai daga hannun ta ke yi amma hankalinta sai ya tafi kan nahge-hangen wasu wurare. Ta yi sauri ta gaya mata cewa, ranki ya dade hankalinki fa ba ya kansu, sannan ta dawo hayyacinta.
Ana cikin haka Asadulmuluuk suka shigo cikin dausayin, ya yi ado da ba irin na samarin kasar ba. Dama Zuhairu yana gaya masa cewa, shi fa yana tsoron kada idon ‘yan matan garin nan ya afka kansa, saboda adon da ya yi. Ai kuwa suna shiga da’irar wurin kallo ya koma kansa, suka samu kasan wata bishiya suka zauna suna hira, a can kuma Gimbiya ta matsu da ganinsa.
Da jama’a suka ragu ita kuma ta gama karbar gaisuwa daga Jama’a, sai ta ga jama’a suna sauri barin wurin kamar dai wani abin mamaki yana faruwa, ta tambayi Ummu Nazifah, shin me yake faruwa ne ta ga Jama’a suna yin tsintsiya zuwa wani wuri daban? Ummu Nazeefah ta nemi izni don ta gano abin da ya ke, faruwa, da zuwanta sai ta ga Asadulmuluuk ake kallo, ta yi mamakin yadda ta ganshi, saboda duk da iya kwalliya da samarin kasarsu da ta hange shi sai ta ga shi ne mafi iya ado a cikin su, dama kuma yanayin launin jikinsa da ban da na mutanen Kasarsu
Ta tsaya tana kallonsa, sai ta ga idan maza sun zo wucewa ta kusa da shi tun suna satar kallonsa, har ya zamto sun kasa daurewa suna kura masa ido. Mata kuma suna kallonsa irin kallo na so da nuna kauna, kamar za su dauke shi daga inda yake.
Ta koma wurin Gimbiya Badee’atulkhairi, ta ba ta labari, “K-a-i! ranki ya dade na ga yarimanki ya yi ado ya yi kyan da kowa ma kallonsa ya ke yi, yalla ko ‘yan matan Askandariya suna tsammanin ma ko Bin Adama ba ne? Ana kallon sa ana kara begensa, abin al’ajabi hatta maza ‘yan uwan ma bai kubuta daga idanunsu ba. Tsarki ya tabbabata ga Ubangijin da kyautata hallitta.”
Gimbiya ta mike tsaye, zuciyarta kamar za ta fashe kishi ya cika, ta sa kafa ta yi fatali da kayan abin da aka kawo mata na sha, ta ce; “ Ummu Nazifa kin cika ni da zancen da bai da fa’ida, Kaicon kwalliyar da zan yi idan bai ganta ba, kaicon zuwana wannan wuri bai ga fuskata ba, ki ba ni labari yalla yana cikin koshin lafiya ko akasin haka?” Ga dukkan alamu yana cikin koshin lafiya a jikinsa, amma cikin fuskarsa akwai damuwa, wannan damuwar ita ce ta alamta min abin da zuciyarsa ke dauke da shi, cewa yana cikin damuwar rashin ganinki.
Za mu iya gasgata kalaman Zuhairu cewa yana cikin mararin son ki, ya’alla ko Shagafu ya mamaye sa, don na ga kamar babu karsashi a tare da shi kamar yadda na sanshi.” In ji Ummu Nazifah. Gimbiya ta ce; “Ya Ummu Nazifah laifi fa namu ne kuma wajibi mu dauki laifinmu, a je a karanta masa gaisuwata a fada masa in yana bukatar ganinmu to ashirye muke mu zo muhallin da yake.” Ummu Nazifah ta ce; “Kalamanki babu ja, ballantana jayayya, amma lokacin da za mu furta hakan ya wuce, tun da fari ya kyautu mu bayyana hakan, ba yanzu da muka shigo filin da ga ba, don haka dole ne mu yi yadda za mu yi.
Ranki ya dade mu fa mata ne cewa aka yi duk mukamin mutum sai ya zo muhallin da muke, a hakan ma sai mun amince da shi, idan kuma ya zo ya samu akasin haka to mun fadi. Mu gode wa Allah da ya sa ba dan wani ne can gefe kika kamu da sonsa a Kasar nan ba. Ki kara hakuri lokaci bai yi ba, in muka yi haka sai talakawanki su hangemu a matakin wawaye, kuma dattakun masarautar Askandariya ya fadi, ki sani cewa kowa ya taru a wannan mhalli ne saboda ke, amma kuma a ga mun taho wurin wani dan sarki wanda ke aka sani shi ba a san shi ba? kai lallai idan muka aikata hakan martabarmu ta fadi kasa, kuma mun nuna kaskancin mu a fili.
Ba zuwanmu wurinsa ne makasudin zuwanmu nan ba, a’a jama’a su ga ya taso ya zo in da muke shi ne makasudin zuwanmu, shin kin ga yadda a ke kallonsa kuwa, ya kamata duk kallon nan da ake yi masa jama’a su ga dama babu wadda ya dace da ita sai ke, a hakan ma kuma su gas hi da kansa ya taso ya zo in da kike, wannan shi ne cikar ‘yancimmu.”
Gimbiya ta koma ta zauna, cikin sanyin magana ta ce; “Haba Ummu Nazeefah, haba Ummu, zuciyata tana bugawa kamar yadda siyasan zinaren da ke jikina suke gugar junansu, kai al’amarin ya wuce haka, ina daf da kamuwa da wata cuta a wannan yanayi na rashin ganinsa, lallai akwai yiwuwar sabunta rayuwata bayan ta duniya nan ba da jimawa ba.” Ummu Nazifah ta ce; “Ya Salaam ban yi tsammanin jin haka daga gareki ba, kina ambaton mutuwa sa’i bai yi ba?.”
Gimbiya ta ce; “ Magana ki ke yi a kan talakawa kada su ga gazawarmu, to idan ba mu gaza ba suna da maganin da za su ba mu na warakar cutar da muka dauka a sababin soyayya? Ni ce nake fama da Shagafu, shi kuwa Hubbu kadai ke cikin ransa.’’ ta sanya ‘yan yatsunta ta dafe goshinta, inda hakan ya lamtawa Ummu Nazeefah cewa kanta ya fara ciwo.
Ana haka sai Zuhairu ya yi sallama, suka amsa gaba dayansu, Ta yi sauri ta saki kanta, aka yi masa iznin shigowa ya shigo, bayan ya yi gaisuwa ya ce; “ Ranki ya dade yarima ne ya ce; “In karanta miki gaisuwarsa, bayan haka yana neman iznin zuwa ya gana da ke na ‘yan wasu dakikoki.” Kafin Gimbiya ta yi magana Ummu Nazeefah ta yi sauri ta tari numfashinta ta ce; “An karbi gaisuwarsa, amma ya dakace mu in mun shirya za mu neme shi.
Gimbiya ta ji kamar ta kantse ta da mari, amma sai ta tuna da alkawarin da ta dauka cewar ba za ta yi mata jayayya ba.” Bayan tafiyarsa Gimbiya Badee’atulkhairi ta fusata ta ce; “Ummu ni fa bana kaunar ganin abin da zai sake fusata Asadulmuluuk, a kan haka zan iya daina ganin dattakunki.” “Ranki ya dade ai wannan lokacin muke jira kuma ya zo, kin manta mun zo nan ne saboda shi da kansa ya zo har muhallin da muke?
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!