Connect with us

RAHOTANNI

Atiku Ya Samu Gaggarumin Tarba A Jihar Kano

Published

on

Tawagar Dan takarar Kujerar Shugaban Kasa Karkashin Tutar Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar tare da Daraktan Yakin Neman Zabensa Dakta Bokula Saraki ta sauka a Kano a ranar Lahadin nan a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano, Alhaji Atiku Abubakar ya samu gagarumar tarba daga Al’umma Jihar Kano musamman Kwankwasawan dake biyayya ga darikar Kwankwasiyya wadda tsohon Gwamnan Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya a halin yanzu Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta.
Tun da farko dan takarar shugabancin Kasar na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya fara ziyartar gidan Marigayai Malam Aminu Kano domin ziyarar girmamawa ga dan Kisihin kasa kuma gogarman kare hakkin talaka Marigayi Malam Aminu Kano. An gudanar da addu’o’I a kabarin Marigayai Malam Aminu Kano, sannan kuma an yiwa Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, Dan Masanin Kano da sauran jama’ar da Jihar Kano ta rasa cikin ‘yan shekaran dasuk gabata.
Bayan kammala ziyarar gidan Marigayi Malam Aminu Kano ne kuma tawagar yakin neman zaben Atiku Abubakar ta wuce zuwa Fadar Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II inda ya kai ziyarar girmamawa tare da neman sa albakar sarkin cikin wannan takarar da ya ke. Alhaji Atiku Abubaka ya bayyanawa Sarkin na Kano cewa ya zo wannan fada mai albarka ne domin neman tabarakin mai martaba sarki bisa wannan aniya tasa, saboda haka sai ya tabbatarwa Sarkin cewa idan Allah ya bashi wannan dama zai yi kokarin sake inganta harkokin masarautun mu kasancewar shima daga cikin masarauta ya fito. Saboda sai ya tabbatarwa da al’umma irin abubuwan alhairin da zai tabbatar idan ya
samu sahalewar Jama’ar Kasa.
Shima ana sa jawabin mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunasi II ya godewa dan takarar shugabancin kasar karkashin tutar Jam’iyyar PDP, sarkin ya ja hankalin masu zabe dasu guji siyasar sayar da kuri’unsu ga wani dan takara, sannan kuma ya bukaci ‘yan siyasa su kaucewa siyasar zubar da jinni, a karashe ya yi addu’ar fatan Allah ya sa ayi zabe lafiya agama lafiya.
Daga Fadar Sarkin na Kano ne kuma tawagar Atiku Abubakar ta nufi filin wasa na Sani Abacha inda dubun dubatar ‘yan Jam’iyyar PDP da kuma ‘yan Kwankwasiyya wadanda yawancinsu ke sanye da jar hula, bayan da Alhaji Atiku Abubakar ya isa filin taron ne wuri ya rude da hargowa ana ta ihun Kwankwasiyya, kwankwasiyya.
Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa day a mik domin gabatar da Jawabisa ga mahalarta taron wanda soya da hargowar masoya ta hana jin wasu daga cikin kalaman wazirin na Adamawa, amma dai ya yi kokarin nuna farin cikinsa bisa wannan karamci, sannan kuma a jinjinawa limamin Kkwankwasiyyar Sanata Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya bayyana da cewa jagora ne mai cikakken kima a idon al’umma. Atiku Abubakar ya ce bai yi mamakin iirn wannan gagarumin gangami ba domin Jihar Kano itace Jihar da ake gwada karfin kowanne dan takara, don haka sai ya tabbatarwa da jama’a musamman ‘yan Jam’iyyar PDP cewar insha Allahu sune zsu lashe zabe nan kwanaki bakwai masu zuwa.
Atiku Abubakar ya bukaci jama\a kowa ya fito domin kada kuri’arsa sannan kuma idan kada kuri’a a kasa, a tsare kuma araka domin ba zamu yarda daduk wani shiri na magudin zabe ba, Akarshe Atiku Abubakar ya bayyana cewa muna sane da irin halin taauci da matsalar tsaro da wasu bagarorin kasar nan ke fuskanta, don haka ina tabbatarwa da al’ummar Nijeriya muna da kwarewar da zamu yi aiki tare da masu kishin kasa wajen kawar da duk wata matsala da ke addabar kasar nan, don haka sai ya bukaci jama’a cewa ayi zabe cikin nutsuwa a guji tad a hankali domin mu masu bin doka da oda ne. Dagan a sai ya godewa jama’a da suka yi wannan dogo jira, wannan kuma ya faru ne sakamakon dandazon al’umma
da suka yi dafifi domin nuna kaunarsu da mubayi’arsu ga jam’iyyar PDP.
Cikin wadanda suka nishadantar da al’umma a wurin wannan taro akwai ‘yan wasan Finafinan Hausa irinsu Adam A. Zango, Sani Danja, sai kuma mawaka kamar shugaban kungiyar mawallafan Kwankwasiyya Tijjani Gandu da Rabi’u Mai Denmark ne suka cashe a wurin taron.
Baba shakka wannan taro ya zo da wani irin al’ajabi domin wasu na ganin taron Atikun ya haura zuwan shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kano a makon day a gabata, musamman idan aka dubi yadda cilon wasan ya yi cikar kwari ba masayar tsinke, baya ga dubun dubatar jama’a da basu samu sukunin shiga cikin filin aron ba suna waje.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!