Connect with us

MANYAN LABARAI

Ba Mu Muka Ba Tsohon Shugaban Bankin Skye Guba Ba —EFCC

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta karyata zargin bai wa tsohon shugaban bankin Skye Bank Mista Tunde Ayeni kuba. Wannan furuci ya fito ne ta bakin mukaddashi jami’an hulda da jama’a na hukumar Mista Tony Orilade, wanda ya yi a garin Abuja ranar Asabar, ya kwatanta zargin a matsayin “Kawo ra’ayi zuga mutane a cikin hukumar EFCC. “Wannan jan hankali ya biyo bayan rahoton Jaridar Thisday na ranar Asabar 9 ga watan Fabrairu, mai taken, “Hukumar EFCC ta bai wa Tunde Ayeni guba a gidan yari.”
“Marubucin wannan rahoton, ya rubuta hakan ne sakamakon tattaunawan da suka yi da kakakin jam’iyyar CUPP Mista Ikenga Ugochinyere, wanda ya gudana a ranar Juma’a 8 ga watab Fabrairu, a garin Abuja.
“Ugochinyere ya yi ikirarin cewa, ya samu bayanai wanda suke nuna cewa a yanzu haka hukumar EFCC ta bai wa Ayeni guba.
“Lokacin da muka samu wannan labara mun yi kokarin kai korafi ga gwamnatin jihar cewa, hukumar ta cafke Ayeni sannan tana kokarin ba shi guba ko dai a cikin abinci ko kuma cikin kayan sha. “An yi kokarin bincikan irin abinci da kuma ruwan da ake ba shi.

“Lokacin da aka yi koranfin cewa ba shi da lafiya yana bukatar ganin likita, da sauri suka kai shi wajen likita.
“Muna sanarwa mutanen jihar cewa, babu wani rahoton rashin lafiyar Ayeni. “Muna bukatar mutane su sani cewa hukumar tana gudanar da aikinta yadda ya kamata kan duk wani wanda ake zargi ba tare da nuna wani bambanci ba.
“Muna sanarwa jam’iyyar CUPP cewa, hukumar tana gudanar da aikinta yadda doka ta tsara. “Domin haka, muna bayyana cewa zargin da ake yi wa Ayeni na cin hanci yana hannunmu muna gudanar da bincike, saboda haka yake wajen mu. “A wannan lamari yana da muhimmanci mu bayyana cewa, hukumar EFCC karkashin jagorancin Ibrahim Magu ba za ta taba kare wani dan siyasa ba, domin tsarin mulki ya ba ta damar a binciki kowa da kowa.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!