Connect with us

Nahiyar Afirka

Ba Zan Ce Komai Ba Kan Sakin Laurent Gbagbo –Ouattara

Published

on

Shugaban kasar Kodebuwa wato Alassane Ouattara ya ce ba zai ce komai dangane da sakin da hukuncin kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya ta yi wa tsohon shugaban kasar, Laurent Gbagbo.

Yayin wata hira ta musamman da RFI, shugaba Ouattara ya ce, ba zai ce komai kan wanke Gbagbo daga zargin da ake yi masa ba, amma kuma ya zama wajibi wani ya dauki alhakin kisan da aka yi wa mutane sama da 3,000 da suka mutu sakamakon rikicin siyasar kasar.

Ouattara ya ce, suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano wanda ke da hannu wajen tashin hankalin da ya yi sanadiyar hallaka dimbin mutanen.

Dangane da murabus din shugaban Majalisar Dokokin Kasar, Guillame Soro daga mukaminsa kuwa, shugaba Ouattara ya ce, babu matsala a tsakaninsu, sai dai bambancin ra’ayin siyasa.

Rahotanni na cewa, Soro wanda tsohon jagoran ‘yan tawaye ne, na takun-saka da Ouattara kuma akwai yiwuwar tsayawarsa takarar shugaban kasa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!