Connect with us

MANYAN LABARAI

Babu Dan Takarar Da Muke Goyon Baya A Nijeriya -Amurka

Published

on

Jakadan kasar Amurka a Nijeriya, Mista Stuart Symington ya musanta cewa kasar Amurka tana goyan bayan wani dan takara ko kuma jam’iyya a babban zabe.
Symington ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wata ziyarar ga gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura a garin Lafiya ranar Asabar.
Ya ce, “Amurka ba ma goyan bayan wani dan takara ko kuma wata jam’iyya a wannan zabe mai zuwa. Tilas Nijeriya ta yi kokarin aiki tukuru wajen gudanar da sahihin zabe kamar yadda zaben shekara ta 2015 ya gudana.
“Ba mu da wani dan takara ko kuma wata jam’iyya, amma muna fatan ‘yan Nijeriya su zauna lafiya tare da gudanar da sahihin zabe. Muna fatan ‘yan Nijeriya su hada kansu wajen yada munufa zuwa makwabtarsu da kuma kasashen duniya baki daya.”
Jakadan ya yi kira ga ‘yan takara su rungumi akidar zaman lafiya, ya bayyana cewa ko wani dan Nijeriya zai yi bayanin abin da ya aikata ko kuma ya yi a gaban Allahi. Ya kara da cewa, “Kowani daya daga cikinmu yana fatan hadin kan Nijeriya, mu dai baki ne, muna alfahari da wannan zabe.”

Shi ma gwamna Al-Makura ya bayyana cewa, gwamnatin jihar za ta tallafa wajen gudanar da wannann zabe. Gwamnan ya bayyana cewa, “Na tabbatar da cewa jihar Nasarawa tana da rawar da za ta taka tare da kungiyoyin kasar waje. Ina kira ga dukkan jam’iyyu su guji mugayen kamamu domin ciyar da kasar nan gaba.
“Duniya tana kallon mu, sannan muna son su kalli abin da muke gudanarwa. Shugaban kasa Muhammadu Buhari tsayar da doka da oda shi ya sa ya samu girmamawa daga kasashin duniya.”
A halin yanzu, shuwagabannin wakilan kungiyar Turai sun iso Nijeriya, jakadar kungiyar kasashen Afirka Ketil Karlsen ya bayyana cewa, ba ma goyan bayan wani dan takara a Nijeriya ko kuma tursasawa ‘yan Nijeriya a kan su zabi wani dan takara. Karlson ya yi wannan furuci ne lokacin da ya kai wa gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ziyara a Yenagoa ranar Juma’a.
Ya kara da cewa, “Mun kawo wannan ziyara ne domin zaben shugaban kasa da kuma na gwamna a Nijeriya, don mu bayyana wa gwamna tare da magoya bayansa muhimmancin gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hanakali a Nijeriya.
“Mun tabbatar da cewa mulkin dimokaradiyya shi ne yafi, domin shi ne yake kara kawo kwanciyar hakali da ci gaba da kuma bai wa talakawa ‘yanci a Nijeriya. Shi ya sa muke kara jadda cewa, kungiyar tarayyar Turai da kuma wasu kungiyoyin kasar waje sun iso Nijeriya ba don su goyi bayan wani dan takara ba.
“Wannan ba zai taba yiyuwa ba kuma ba ma fatan haka. Abin da muke bukata shi ne a gudanar da sahihin zabe a cikin wannan kasa.”
Dickson ya yaba wa kungiyar kasashen Turai da sauran kungiyoyi a kan aikinsu na ci gaba da kuma kwanciyar hankali cikin wannan kasa. Ya kara da cewa gwanatin jiha Bayelsa ta amfana da wannan aiki. Dickson ya ce, jihar tana kokarin ganin an yi sahihin zabe cikin kwanciyar hankali, kuma hakan zai gudana ne idan an yi aiki da ka’idojin zabe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!