Connect with us

WASANNI

Bayan Man City Sun Lallasa Chelsea Ci 6 Da Nema, Kujerar Sarri Na Rawa

Published

on

Kociyen kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Maurizio Sarri ya ce, aikinsa na horaswa na fuskantar barazana a kungiyar Chelsea bayan lallasar da suka sha a hannun Manchester City da ci 6-0 a gasar firimiyar Ingila.

Wannan shi ne karo na farko tun shekarar 1991 da Chelsea ta sha wannan  mummunan bugu a hannun wata kungiya a gasar Firimiyar Ingila, in da a wancan lokaci, Nottingham Forest ta lallasa ta  da ci 7-0.

Sarri da kaftin din Chelsea, Cesar Azpilicueta sun bai wa magoya bayan kungiyar hakuri kan lallasar da suka sha a hannun Manchester City a Etihad, abin da ya rikito da  kungiyar zuwa mataki na 6 a teburin gasar.

Sargio Aguero ya sake taka muhimmiyar rawa a fafawar ta ranar Lahadi, inda ya jefa kwallaye uku shi kadai, yayin da Manchester City ta sake komawa saman teburin gasar da maki 65, in da sake karbe ragama daga hannun Liverpool.

Ita ma Kungiyar Tottenham ta yi nasara akan Leicester City da ci 3-1.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: