Connect with us

SIYASA

Dogara Ya Yi Alkawarin Kammala Ayyukan Da Ya Faro

Published

on

Yakubu Dogara, wanda shi ne dan takarar majalisar wakilai ta kasa a karkashin jam’iyyar PDP, ya shaida cewar muddin al’ummar mazabarsa ta Dass, Tafawa Balewa da Bogoro suna son a karasa musu dukkanin aiyukan da ya faro da wasu karin aiyuka su sake zabinsa a karo na hudu.
Yakubu wanda ke wannan furucin a lokacin kaddamar da yakin neman zabensa a ranar Alhamis a kauyen Dull, ya shaida cewar sun zo da kishin jama’ansu da kuma neman kawo ci gaba, ya shaida cewar sake samun damarsu ne kawai zai bayar da damar a samu nasarar karasa aiyukan da suka faro a yanzu haka, ya ce idan jama’a ba su zabe shi ba, za a samu jinkirin aiyukan gaya.
“Kun ga irin aiyukan da muka kawo, musamman zaman lafiya, duk wani ci gaban da za a kawo muddin babu zaman lafiya to ci gaban ba zai samu, in ba a zaman lafiya ko an samu ci gaban za a zo a rusar da su, duk wanda zai zo ya yi kokarin a zabesa don ya kawo tashin hankali bai kamata ya zama shugaba ba a wannan yankin a yanzu, duk wanda zai kawo ci gaba shugaba na kwarai ya kamata ya hada kan jama’a ne, duk wanda ka ji na kawo batun addini da bangaranci na son a zabe shi ne kawai ya yi gaba,” Inji shi
Dogara ya tabo nasarorinsa, “Babban abun da muka samu a cikin wannan tafiyar, shine zamana Kakakin majalisar tarayya, da kokarinku ne muka kai wannan matsayin sai kuma Allah ya sa mana albarka yanzu ga aiyukan da muke samarwa. Ga aiyukan shimfida tituna da muke yi da ya tashi daga Sum ya biyo ta nan Dull zuwa Burga, akwai aikin titin da muke yi a bayan Dutsen Dass wanda kowa ya sani, akwai wanda zai fito daga can Fanshin ya je ya hado har da kasan Mangu ta can a Gindiri wadannan kusan sune manya-manyan aiyukan da yanzu haka muke yi.
“Wadannan aiyukan da za a kiyasce kudaden da za a kashe za su kai biliyan 46, ina son na bamu tabbacin da gwamnatin jihar Bauchi ce za ta yi wadannan aiyukan sai an shafe shekaru 60 ba a yi ba wanda yawancinmu kila sai mun bar duniya kafin a yi, amma a bisa kokarin da ake yi yanzu kuna gani aikin nan har ya kusa da Kandun da yardar Allah hanyar nan za ta shigo har Dull,” Inji Dogara
Yakubu Dogara ya shaida cewar mafiya yawan aiyukan da yake yi, yana yi ne domin cika alkawuran da ya dauka wa al’umman da ya je wajajensu neman kuri’u, “Yau ga shi na cika alkawuran da na dauka. Aikin hanyoyi ana kai, ga shi na wannan yankin daga nan ana sunsunar hanyar nan. muddin ba ku zabe mu ba zan tabbatar muku yadda aikin hanyar nan ya tsaya haka aikin zai tsaya sai lokacin da wani ya sake zuwa matsayin da nake kafin a sake dago aikin nan, na cika nawa alkawarin na samar da aiyukan sauran ya rage mana ni da ku,” Inji shi
Dogara ya ce, daga cikin alkawarin da ya yi wa jama’an Dull har da samar musu da sabis din na’urar sadarwa, inda ya shaida cewar cikin rashin sa’a sai ya bayar da kwangilar aikin a hanun wani wanda ya ci amanarsa amma ya sha alwashin cewar za a yi musu nan ba da jimawa ba.
Yakubu Dogara ya yi tsokaci kan halin da Nijeriya take ciki a yau, ya shaida cewar Nijeriya tana cikin wani mawuyancin hali a karkashin Buhari, ya ce ba wai suna kin Buhari ne a bisa radin kashin kai ba, illa domin kishinsu da son ci gaban Nijeriya ya fi soyayyar da suke yi wa Buhari a bisa hakan ne ya nemi jama’an kasar da su zabi Atiku Abubakar a zaben da ke tafe domin ya ceto Nijeriya daga halin da yake ciki a yau.
Dogara ya nuna gwamnatin jihar Bauchi mai ci a yau da cewat ta gaza wajen kyautata rayuwar jama’am jihar, inda ma ya yi zargin cewar gwamnan jihar Bauchi ya shigo da wasu baki wadanda suke jan ragamar jihar a maimakon ya kawo‘yan jihar su mori arzikin jihar,“Ko wani alfarma kake nema sai ka je wajen wani wai Ali Kumo, don rainin wayo ko don ya nuna yana son jihar Bauchi a maimakon ya canza zuwa Ali Jama’are ko Ali Tafawa Balewa ko Dass, amma wai sai ka je Kumo kafin a yi maka alfarma a jihar Bauchi abun kunya ne wannan, ko kuma ka je Kano wajen wani kafin a maka alheri a gwamnatin Bauchi,” Inji Dogara
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: