Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Za Ta Cafke Attajirai 85,000 Dake Kin Biyan Haraji

Published

on

Shugaban Hukumar tara haraji ta kasa FIRS Mista Tunde Fowler ya sanar da cewar, hukumar tarae da hadin gwaiwa da wasu masu ruwa da tsaki kamar rundunar yan sanda ta kasa a cikin wannan shekarar zata fara farautar hamsakan masu kudi dake kasar nan da suke kin biyan haraji. Fowler ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a garin Abuja a lokacin da Shugaban yan sanda na kasa na riko, Mohammed Adamu ya kai masa ziyara a ofishin sa dake Abuja.Shugaban wanda ya sanar da hakan a cikin sanarwar da Hukumar ta fitar ya shedawa shugabn na yan sanda cewar, Hukumar tuni Hukumar ta tarawa gwamnatin tarayya bashi naira biliyan 23 daga cikin masu kin biyan harajin har su 45,000 kuma wasu daga cikin su sun biya bashin sama da naira miliyan 100.Ya kara da cewa, Hukumar zata kuma fara farautar wasu hamsakan da suka ki biyan harajin har su sama da 40, 000 a 2019, indaya roki rundunar yan sandan ta kasa data taimakawa Hukumar don samun nasarar karbo harajin daga gun wadanda suka ki biya.Ya ci gaba da cewa, muna son yin hadaka da yan kasuwa da suke samun ribar data kai daga naira miliyan 100 zuwa naira miliyan 999, tuni kuma muka yi nazari akan kasuwancin. Acewar sa, “akawai bankuna kimanin bakawai da har yanzu muke jira don sabunta bayanan su., inda a yanzu muke da guda 45,361 da suka mallaki shedar su ta (TIN) kuma suna biyan kudi.”Mista Tunde Fowler ya ce, wanda suka mallaki TIN dinsu su 40,611 sun biya harajin su kuma muna da guda 44,504 da basu da shedar TIN kuma basu biya harajin su ba, inda ya ce, idan kayi dubi zaka gamuna da kusa da. 75,000 a cikin wannan rukunin da har yanzu basu biya harajin sub a kuma mun sha fada cewar, biyan haraji ba sai ma’aikacin gwamnati kadai ba abune da ya dace dukkan yan kasa su dinga biya.Fowler ya kuma yabawa rundunar ta yan sanda ta kasa akan gudunm,warar da suke baiwa hukumar sa tare da kuma hadakar da hukumar tayi da rundunar don tallafa mata wajen cin nasarar ta hara harajin da ta sanya a gaba don samun kwato harajin daga gun hamshakan dake kasar nan a cikin shekarar 2019.Yayi nun da cewar, bad an yan sandan ba, ina mai kwankwanton in har hukumar zata iya samun cin nasarar dat samu na tara harajin a shekarar 2018. Ya ce, hukumar ta samu nasarar tara harajin jimlar naira tiriliyan 5.32 wanda wannan shine mafi yawa a tarihin hukumar.Shi kuwa Shugaban yan sanda na kasa na riko, Mohammed Adamu Adamu ya ce, rundunar zata ci gaba da baiwa hukumarhadin kan da ya dace, inda ya ce, domin tara harajin wani faffni ne babba na ciyar da kasar nan a gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: