Connect with us

WASANNI

Harry Kane Ya Gama Kulla Yarjejeniya Da Real Madrid

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Harry Kane, dan kasar ingila, ya cimma yarjejeniya da kungiyar Real Madrid kan sauya sheka zuwa kungiyar idan aka bude kasuwar siye da siyar da ‘yan wasa ta gaba.
Shahararriyar mujallar labaran wasanni ta kasar Sipaniya ‘Don Balon’ ta rawaito cewa Harry Kane ya amince ya rattabawa Real Madrid hannu kan yarjejeniyar buga wasa na tsawon shekaru biyar.
Sai dai an cimma matsayar ce tsakanin dan wasan da wakilan Real Madrid, yayin da a yanzu ya rage, tattaunawa tsakanin Real Madrid din da kuma kungiyar Tottenham kan farashin Harry Kane.
An dai shafe watanni ana alakanta Harry kane da sauya sheka zuwa Real Madrid tun bayan da tauraruwarsa ta dada haskawa a fagen zura kwallaye a raga bayan da dan wasan ya lashe kyautar gwarzon dayafi yawan zura kwallo a raga a gasar firimiya sau biyu a jere.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai ta ware kudade masu yawa domin yin garambawul a kungiyar wanda hakan yasa kungiyar take neman shahararrun ‘yan wasa domin kara karfin da zata takawa Barcelona birki.
Kungiyar dai tana fama da rashin zura kwallaye a raga sakamakon dan wasan gaba na kungiyar, Karim Benzema baya zura kwallaye a raga yadda yakamata wanda hakan yasa kungiyar take ganin akwai bukatar siyan babban dan wasan gaba.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ma tana zawarcin dan wasa Harry Kane wanda akafi tunanin zai koma Real Madrid domin maye gurbin Cristiano Ronaldo wanda yabar Real Madrid a kakar wasan data gabata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: