Connect with us

LABARAI

Hukumar JAMB Ta Shirya Tsaf Don Gudanar Da Jarabawar UTME

Published

on

Hukumar da take shirya jarabawar shiga manyan makarantun Nijeriya, wato UTME, ta ce a shirye take tsaf don gudanar da jarabawar UTME din kamar yadda saba a duk shekara, hukumar ta bayyana hakan ne yau Litinin a garin Abuja.

Bayan gama tantance irin shirye-shiryen da hukumar ta yi, da kuma kayan aiki da ta tanada, inda ta gabatar da su gaban kwamitin da yake da alhakin tantance shiri da kuma kayan aikin da hukumar ta tanada don gudanar da jarabawar cikin nasara a ranar 6 ga watan Fabrairun nan da muke ciki.

Hukumar ta tabbatar da cewa ta shirya tsaf don gudanar da jarabawar ta wannan shekarar, kuma zuwa yanzu komai yana nan yanda ta tanada, sannan tsarin da ta fitar na yin rijista a wannan shekarar ya kayatar fiye da tsare-tsaren da ta yi  a baya.

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya gabatar wa da kwamitin duk tsare-tsaren da hukumar ta yi, a ranar 10 ga watan Junairun da ya gabata hukumar ta bude shafin rijista a yanar gizo, inda ta baiwa kowa damar yin rijista har zuwa ranar 21 ga watan Fabrairun nan da muke ciki.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!