Connect with us

SIYASA

Ibrahim Mantu Ya Shawarci ‘Yan Siyasa Da Su Sauya Halayyarsu  

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa wato Sanata Ibrahim Mantu, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su sauya halayensu wajen ganin an bunkasa tafiyar dimokradiya a kasarnan, a yau Litinin.

Mantu, wanda yake daya ne daga cikin kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ya yi wannan kiran ne a lokacin wani bukin kaddamar da wani littafi mai taken; “The Legacy of Atiku Abubakar on Nation-Building.” Littafin wanda Rabaran Chukwudi Eke, Babban mashawarci akan harkokin siyasa ga gwamnan jihar Delta wato Ifeanyi Okowa.

Mantu, ya ce; an fuskanci Dimokradiyya a kasarnan daga shekarar 1999 zuwa  2019, ya ce; ya zuwa yanzu ya kamata a ce an samu ci gaba ne sosai. Ya ci gaba da cewa; abin bakin ciki ne a ce har yanzu Nijeriya ba ta tafiya akan gwadaben dimokradiya. Ya ce; hatta jam’iyyun siyasa ba sa tafiya kan gwadaben dimokradiyya. A nan ne ya shawarci ‘yan’uwansa ‘yan siyasa da su sauya halayyarsu domin sam halin na su na yanzu bai kawo kasar ci gaba ba, ya kara da cewa; lokaci ya yi da ya kamata a ci gabantar da Nijeriya.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: