Connect with us

LABARAI

INEC Ta Fitar Da Samfur Din Akwatin Zaben 2019

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta saki samfurin hotunan akwatin zaben da za’a yi amfani da su a zabukkan 2019, Akwatinan zaben na da kaloli daban-daban, inda ko wanne kallan akwati yake bayyana.

Jan akwati shine na shugaban kasa, bakin akwati kuma na yan majalisar dattawa, shi kuma koren akwati na majalisar wakilai. Dukkkan zabukan guda uku za’a yi su ne ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu, 2019.

Sauran zabukan za’a yi su ne ranar 2 ga watan Maris 2019, inda shima jan akwati shine na gwamnoni shi kuma bikin akwatin shine na majalisar jiha. Suma wadannan zabukan za’a yi su rana daya, INEC ta fitar da wanan bayanin ta shafin ta na twitter.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!