Connect with us

KASASHEN WAJE

Iraniyawa Sun Yi Wa Amurka Kwalelenki  A Yayin Bukin Cikar Juyin-juya Hali Shekaru 40

Published

on

Dubbunan al’ummar kasar Iran ne suka fito akan manyan titunan biranen kasar ta Iran, don murnar bukin cikar juyin-juya halin musulunci shekaru 40, Iraniyawan suna murnar cikar kasar shekaru 40 a karkashin tsarin musulunci ne, tun bayan da shugaban addini na kasar Ayatullahi Khumaini ya jagoranci kifar da gwamnatin Shah.

A ranar 11 ga watan Fabrairun shekarar 1979 ne al’ummar kasar Iran din suka samu nasarar korar Sarki Shah, wanda cikakken dan barandan Amurka da kasashen yammacin turai ne, daga karagar mulkin kasar, duk da kasashen Amurka din sun yi ta goyon bayan Shah din, amma hakan bai hana al’ummar kasar korar shi daga karagar mulki ba.

Tarin dandazon Iraniyawan ne suka yi dafifi a kan manyan tituna, duk da matsanancin sanyi da ake fama da shi da ma dusar kankara da take sauka, Iraniyawa suna ta rera taken, mutuwa ga Amurka, mutuwa ga Isara’ila, wannan taken da shi al’ummar kasar suka samu nasarar tunbuke Sarki Shah daga karagar mulkin kasar shekaru 40 da suka wuce.

A yayin jawabin shi, shugaban kasar Iran din, Hassan Rouhani ya ce; takunkumin da kasar Amurka take kakkabawa kasar Iran bashi da wani tasiri wajen rusa kumajin al’ummar Iran din, sai dai ma ya kara musu jajircewa da kara tsanar manufofin kasar ta Amurka akan kasar su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!