Connect with us

LABARAI

Jami’ar Ilorin Ba Za Ta Lamunci Ayyukan Kungiyar Asiri ba –Rijistara  

Published

on

Rijistaran jami’ar Ilorin dake jihar Kwara, Dakta Folaranmi Olowoleni, ta gargadi dalibai cewa sam-sam jami’arsu ba zata lamunci ayyukan ‘ya’yan kungiyar asiri da tahamulli da miyagun kwayoyi a cikin jami’ar ba, Olowoleni ta bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake taron maraba da sabbin daliban da suka shigo makarantar.

Ta kara da gargadin daliban da su kiyaye satar amsa a lokutan jarabawa, sannan su dinga shigar mutumci zuwa makaranta, ta shawarci daliban da su kasance masu aiki tukuru, sannan su bi dokokin makarantar sau da kafa, domin ta hakan ne kawai zasu cimma nasara kamar yadda ya dace.

Itama mataimakiyar shugaban jami’ar, Farfesa Sylvia Malomo, ta bukaci dalibai da su kasance masu halaye na gari abun koyi, sannan su kasance masu tsumi da tanadi, su daina yin almubbazaranci da kudadensu, su guji abubuwa marasa kyau, misali caca da sauran nau’in abubuwa irin cacar.

Shugaban harkokin dalibai shima ya shawarci daliban hanyoyin da zasu bi don cin nasara a karatunsu, sai babban limamin masallacin jami’ar shima yayi wa daliban nasiha mai ratsa zuciya, takwaranshi na addinin kirista shi ma yayi wa daliban nasiha kamar dai yadda sauran masu jawabi suka yi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: