Connect with us

RAHOTANNI

Kafin Ranar Zabe Za A Bayyana ‘Yan Takarar APC Na Zamfara, Inji Shugaban Kasa

Published

on

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa, kafin ranar zabe hukumar zabe za ta bayyana ‘yan takarar APC na jihar Zamfara. Shugaban kasar ya bayyana haka ne jiya wajen yaki neman zabensa a jihar Zamfara.
Shugaban kasar ya bayyana nasarorin da ya samu a harkar tsaro a gabashin Nijeriya, da kuma bunkasa noma wanda yanzu haka an daina shigo da shinkafa daga waje, ta cikin gida ake ci .
Kuma ya jadda cewa, za a yi titin jirgin kasa ya zarce da zai zarce zuwa Sakkwato, kuma batun cin hanci da rashawa kuwa koto ce ke kawo ikon hukunta su, don yanzu ba lokacin soja bane, lokacon ina soja kamasu nayi na dauri yanzu kuwa dole sai kotu ke da wannan hurumin,” inji shi.
A nasa jawabin Shugaban Jamiyyar na kasa Kwamarad Adam Ashinomole ya bayyana cewa, gwamnatin jamiyar APC, ta yi rawar gani a shekarun da ta yi, kuma yanzu haka akwai shiri na musamman don ci gaban kasar nan.
Da ya koma kan ‘yan takara su da hukumar INEC taki amsa ya bayyana cewa, Allah yafi karfin INEC, kuma koto ma tafi karfin INEC, tunda kotu ta ba INEC damar ta amsar ‘yan takara mu ya zama dole a amsa kuma da yardar Allah kafin lokacin zabe za ta amshi ‘yan takara.
A nasa jawabin mai masaukin baki Gwamna Yari ya tabbatar wa da Shugaban kasa cewa, tun daga shekara ta 2003 Shi ke cin zabe a Zamfara, wannan shekara ma haka ya ke babu canji, kuma abun da yasa Shugaban Kasa ba zai bada tuta ga ‘yan takara ba shi ne don lamarin na koto shi kuma mai bin umarnin koto ne, amma da yardar Allah nan bada jimawa ba za a bayyana su.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Lawali Liman Kaura ya bayyana godiyar sa ga tawagar shugaban kasa.
Kuma ya bayyana nasarorin da Gwamnatin jjhar Zamfara ta samu hawan mulkin Gwamna Yari ya zuwa yanzu, kuma shi shugaban Kasar sheda ne don ya halarci bude wasu ayyukan da gwamna Yari ya gabatar kuma wadannan ayyukan sune karfin gwiwar mu na cin zabe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!