Connect with us

LABARAI

Kamfanin Tumatur Na Dangote Na Gab da Fara Aiki

Published

on

Kamfanin tumatur na Dangote wanda yake Kadawa cikin jihar Kano, wanda ya dai na aiki fiye da shekara daya, sai ci gaba da aiki cikin mako biyu masu zuwa. Shugaban kamfanin Alhaji Abdulkarim Kaita shi ya bayar da wannan tabbaci a wata hira da kamfanin dillancin lamarai na kasa ranar Asabar a jihar Kano. “Za mu dawo gudanar da aiki a cikin mako biyu masu zuwa. Wannan shi ne shirinmu idan Allah ya yarda,” in ji shi.
Kamfanin dillanci labarai na kasa ya ruwaito cewa, tun da farko kamfanin ya daina aiki ne sakamakon barnan Tuta, wanda ya yi sanadiyyar yi wa manomar jihar Kano barna a cikin shekaru biyu da suka gabata. Duk da haka, lokacin da kamfanin yake gudanar da aiki a shekarar 2017, kamfanin ya tsaida gudanar da aiki sakamakon karanci tumatur wanda manoma tumatur suka samu a jihar. Ya bayyana cewa kamfanin ya gana da manoma tumatur na jihar, inda aka tattauna da su yadda za su yi kokarin kawo wa kamfanin tumatur.
Kaita ya ce, a ziyar da suka kai wa gwamnan babban bankin Nijeriya Gadwin Emefele da kuma ministan gona Cif Audu Ogbeh su tabbatar musu da cewa gwamnatin tarayya ta haramta shigowa da tumatur cikin wannan kasa. “Lokacin wannan ziyara wanda kamfanin ta kai wa wadannan jami’ai guda biyu, sun tabbatar mana da cewa gwamnatin tarayya za ta bayar da cikakkiyar boyan bayan shirin tumatur a cikin wannan kasa. “Muna fatan gwamnati za ta cika wannan alkawarin domin kara karfafawa manomar tumatur gwarin giwa su kasance cikin wannan kasuwanci,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano ta yi kokarin cika alkawarin da ta dauka wajen karawa manomar tumati gwarin giwa domin su noma tumatur mai yawan gaske. “Lokacin wannan ziyarar, jami’an gwamnatin tarayya sun tare da mataimakin gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Gawuna da kuma gwamnan jihar sun yi alkawarin karfafawa manomar tumatur gwarin giwa.”
Kamfanin dillancin labarai na kasa ta ruwaito cewa kamfanin zai iya sarrafa ton 120 na danyen tumatur a kullum.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!