Connect with us

WASANNI

Ko Pogba Zai Koma Real Madrid?

Published

on

Rahotanni daga kasar ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta tuntubi Manchester United ko zata iya siyar mata da dan wasanta Paul Pogba domin yakoma kungiyar a kakar wasa mai zuwa.
Pogba, wanda yakoma Manchester United daga kungiyar kwallon kafa ta Jubentus dake kasar Italiya rahotanni sun bayyana cewa yayi rikici da tsohon mai koyar da ‘yan wasan kungiyar, Jose Mourinho wanda hakan yasa aka fara rade radin cewa dan wasan zai iya barin kungiyar.
Sai dai tun bayan da kociyan kungiyar na rikon kwarya yazo kungiyar dan wasa Pogba ya canja inda kawo yanzu ya zura kwallaye da dama sannan ya taimaka an zura kwallaye hakan yasa ake ganin yanzu zai iya canja shawara.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ware zunzurutun kudi sama da fam miliyan 500 a kakar wasa mai zuwa domin yin garambawul a kungiyar sakamakon rashin buga abin azo agani da kungiyar tayi a wannan kakar.
Tuni aka bayyana cewa Pogba yana daya daga cikin ‘yan wasan da kungiyar zata nema domin kara karfi sai dai dole zata fuskanci kalubale kafin Manchester United ta amince da siyar da dan wasan wanda yafi kowanne dan wasa tsada a kungiyar a lokacin data siyeshi fam miliyan 83 daga Jubentus din Italiya.
Sannan Real Madrid tana bukatar ta ware kudi kusan fam miliyan 150 domin siyan dan wasan wanda ya wakilci kasar Faransa ta lashe gasar cin kofin duniya wanda aka fafata a kasar Rasha kuma kamar yadda wani rahoto ya bayyana dan wasan baya son barin kungiyar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: