Connect with us

KASUWANCI

Kungiyar Masu Yin Bulo Sun Yaba Da Sabon Simintin Dangote

Published

on

Kungiyar masu mulmula Bulo ta kasa BMAN sun yabawa rukunonin kamfanin Dangote bisa samar da Siminti mai inganci a kasar nan. Shugaban kungiyar reshen Suleja cikin jihar Nija Cif Patrick Markuche ne ya yi yabon, inda ya danganta sabon Simintin a matsayin mai inganci sosai da kuma samar masu da dimbin riba ga sana’ar tasu. Shugaban ya sanar da cewa, yayan kungiyar sun yi na’am da sabon Simintin harda yiwa kamfanin mubayi’a.Acewar sa, munyi amfani dashi mun kuma gano cewar yana da inganci sosai mun kuma ji dadi a kan samar da shi. Shugaban ya yi nuni da cewa, koda damina yin amfani da sabin simintin akwai inganci. Har ila yau, a cikin sanarwar da kamfanin siminti na Dangote ya fitar a ranar Lahadin data wuce, wani mai rabar da simintin Alhaji Mukhtar Moriki na kamfanin Albabelo masu mulmula bulo sun nuna bukatar da a samar masu da simintin mai yawa. Daraktan sayarwa da raba simintin na Dangote na kasa Adeyemi Fajobi,ya sanar da cewa, sabon simintin an sarrafa shi ne tsaf kuma yana daya daga cikin matakan da kamfanin ya dauka don inganta kaykn sa. Acewar sa, abikan cinikayyar mu suna jin dadin yin amfani da sabin simintin da kamfanin ya sarrafa musamman saboda ingancin sa da kuma yadda suke iya sayen sa da samar masu da riba mai yawa kuma a yanzu a kasar nan, shine mafi inganci da akafi yin amfani dashi. Ya sanar da cewa, wannan simintin ya kai karkon kashi hamsin bisa dari kuma bayan kwana daya yana kara yin karkon da ya kai kashi sha biyar bisa dari, inda kuma yake kara yin karfi bayan kwanuka ashirin da takwas hakan kuma ya sanya masu siye don su siyar da kuma masu yin amfani dashi suke jin dadin yin aiki dashi. A karshe Fajobi ya ce, sabon simintin mai suna BlocMaster an samar da shine bayan bincikn shekara daya da aka gudanar. Yana da inganci da kuma dakile yin asara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!