Connect with us

LABARAI

Ma’aikatan INEC Za Su Yi Rantsuwar Yin Adalci A Zaben 2019

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na cigaba da kara kaimi wajen ganin sun gudanar da zaben bana, a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Nijeriya, yau ne ma’aikatan INEC din za su yi wata rantsuwar aiki, hukumar INEC ta bayyana cewa, a yau Litinin 11 ga watan Fabrairu manyan ma’aikatan hukumar INEC za su yi rantsuwar yin aikin su kamar yadda dokar aiki da kuma tsarin mulkin kasa ya tanada.

Farfesa Francis Chukwuemeka Ezeonu, wanda shi ne babban kwamishinan zabe na jihar Imo, ya bayyana cewa a yau ne ma’aikatan su za su yi rantsuwa tare da kuma sanin aikin da za su yi a zaben da za ayi kwanan nan. Ezeonu ya kuma kara da cewa jami’an zaben za su abin da doka ta tanada ga duk wani jami’in zaben da ya ci amanar aikin da ke kan sa.

Ezeonu yayi bayani ne ta hannun Mai magana da yawun INEC. Jami’ar yada labarai a yankin, Emmanuela Okpara, tace dole ma’aikata su yi aiki ba tare da nuna son kai da banbancin ba. Wannan dai shi ne dalilin tara ma’aikatan su rantse da yin adalci a zaben kasar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: