SIYASA
Ma’aikatan Jihar Kwara Sun Yi Mubaya’a Ga PDP

Gamayyar kungiyoyin ma’aikata na jihar Kwara sun ayyana cikakken goyon ga jam’iyar PDP a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaben kasa tare da fara wad a dzabe shugaban kasa dana majalisar tarayya a ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu 2019.
Maia’katan sun bayyana goyon bayan nasu ne ga dukkan ‘yan takarar ja’iyyar PDP a zaben dake tafe a taron da gwamna jihar, Alhaji Abdulfatah Ahmed ya jagoranta a garin Ilori ranar Litiini.
Cikin wadanda suka halarci taron hard a dab rataarar kujerar gwamna na jam’iyyar PDP, Hon. Razak Atunwa tarebda wasu manyan ‘yan jam’iyyar a jihar.
A jwabinsa, Gwamnan jihar, Ahmed ya bayyana shirin gwamnatin jihar na fara aiwatar da biyan mafi karancin albashi na naira 30,000 ga ma’aikatan jihar.
Ya kuma bayyana cewa, gwamnatinsa ta fara biyan bashin albashin wata daya ga ma’aikata da ‘yan fansho na kananan hukumomi da na jihar gaba daya.
Kungiyoyin ma’aikatan da suka samu hakartar taron sun hada da ‘Nigeria Labour Congress (NLC)’ da ‘Trade Union Congress (TUC)’ da ‘Joint Negotiations Council (JNC)’ da sauran kungiyoyin kwadago a sassaan jihar, sun kuma yanke hukuncin goyon bayan dukkan ‘yan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2019.
Wadana suka sanyan hannu a kan takardar yarjejeniyar sun hada da Yekini Agunbiade na (NLC) da Nasir Olumo na (TUC) da Salihu Sulyman na (JNC) da Toyin Salihu na (NUT) da Yusuf Salihu na (NULGE) da kuma Seidu Oladimeji na kungiyar (NUP).
-
HANTSI2 days ago
Atiku Barazanar APC
-
RAHOTANNI1 day ago
Ba Mu Da Masaniyar Cafke Wani Da Sakamakon Zabe Na Bogi A Abia, Cewar ‘Yan Sanda
-
MANYAN LABARAI2 days ago
Dage Zabe: Ka Da Mu Karaya Akwai Fata –Saraki Ga Al’ummar Nijeriya
-
KASASHEN WAJE13 hours ago
Mayakan Boko Haram 187 Sun Ajje Makamai A Kamaru
-
BUDADDIYAR WASIKA1 day ago
Baba Buhari, Mu Na Murna Da Tazarce
-
LABARAI2 days ago
Dage Zabe: Ba Karamin Mamaki Abun Ya Bani Ba –Atiku
-
LABARAI12 hours ago
Wani Kusa A APC Ya Fice Daga Jam’iyyar A Bauchi
-
MANYAN LABARAI1 day ago
Ko A Dage Zabe Ko Kada A Dage Sai Mun Kayar Da Buhari, In Ji Kera