Connect with us

MANYAN LABARAI

Ma’aikatar Wuta Ba Ta Da Labarin Wasu ‘Yan Kwangila Da Suka Gudu –Fashola

Published

on

Ministan Hasken Lantarki, Ayyuka da Gidaje, Mista Babatunde Fashola ya ce, Ma’aikatar na shi ba ta da masaniyar wasu gurbatattun ‘yan kwangila da suka tsere da kudaden gwamnati ba tare da sun aiwatar da ayyukan da aka ba su ba.
Ministan ya fadi hakan ne a cikin takardan da ya rubutawa kungiyar hana cin hanci da rashawa, kungiyar kare tattalin arziki da kungiyar bin diddigi, a ranar 27 ga watan Janairu.
A makon da ya gabata ne kungiyar ta SERAP ta shigar da Fashola kara a babban kotun Legas, inda take neman a tilas ta shi ya wallafa sunayen ‘yan kwangilan da ake zargi da cin kudin ma’aikatar amma suka tsere.
Kungiyar ta ce, ta yanke shawarar maka Ministan a Kotu ne bayan zargin da take yi na yin watsi da neman da ta yi wa Ministan na ya bayyana sunayen ‘yan kwangilan da suka gudu.
Cikin sanarwar da mataimakin daraktan kungiyar ta SERAP, Kolawole Oluwadare, ya fitar a ranar Lahadi tana cewa, ta sami wasikar da Fashola din ya rubuta mai kwanan wata 27 ga watan Janairu, ne a ranar 7 ga watan Fabrairu, bayan ta shigar da karan a Kotu.
Sanarwar wacce Daraktan harkokin shari’a na Ma’aikatar, Shoitan A.A., ta sanyawa hannu a madadin Ministan tana cewa, “An umurce ni da na sanar da ku cewa mun sami wasikar ku mai kwanan watan 4 ga watan Janairu, 2019, wacce a cikinta ku ka nemi da mu bayyana maku sunayen ‘yan kwangila da kamfanonin da ake zargi da cin kudin gwamnati a kan za su aiwatar da wasu ayyukan lantarki, amma ba su aiwatar da ayyukan ba.
“Mun duba duk takardun bayanan Ma’aikatar a kan bayanan da ku ka nema, amma ba mu sami wadannan bayanan ba.
Sai dai, Kungiyar ta SERAP ta ce, ba ta gamsu da amsar da Fashola din ya ba ta ba, don haka, sai ta umurci Fasholan “da ya dauki duk matakan da suka kamata wajen samun wadannan bayanan daga kowace irin hukuma ne da take da wannan bayanin, ya kuma aike mata da shi ba tare da bata lokaci ba.”
Ta bukaci Fashola da kar ya jira har sai Kotu ta tilasta ma shi da ya amsa bukatar nata na bayyana mata sunayen gurbatattun ‘yan kwangilan da ke aiki a ma’aikatar na shi.
SERAP ta mika wannan bukatar ne bayan zargin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi na cewa, wasu ‘yan kwangilar da aka baiwa ayyukan lantarkin sun gudu bayan kuma an biya su kudaden aikin bakidaya.
“Kudaden sun halaka. Har yanzun, ba dan kwangilan da aka kama. Mutane sun karbi kudaden aikin duka amma sai suka yi layar zana, ba aikin da suka yi,” in ji Atiku, a wani shiri na gidan talabijin na Channels.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: