Connect with us

KASUWANCI

Moghalu Zai Zuba Jarin Tiriliyan Daya A Fannin Fasaha

Published

on

Dan takarra kujerar shugaban kasa a karkashin Jamiyyar YPP Farfesa Kingsley Moghalu ya sanar da zai zuba naira tiriliyan daya don samar da kasuwancin fasaha a Nijeriya in har an zabe shi shgugaban kasa. Moghalu ya sanar da hakan ne a loacin muhawaar da ya yi da masu mastakaitan sana’oi da kuma kafafen yada labarai a jihar Legas. Acewar Kingsley Moghalu kudin zasu kasance ne a matsayin hadaka a tsakanin gwamnati da masana’antu amsu zaman kasnu, inda gwamnatin sa za ta samar da naira milliyan 500 suka kuma masana’antun za su samar da naira miliyan 500. Ya ce, gwamnatin sa ce za ta lura da kudi, inda masana’antun zasu tattabatar da rabar da kudin ga yan Nijeriya, musamman don a rage matsalar rashin aikin da ya addabi kasar nan. Farfesa Kingsley Moghalu ya kara da cewa, in har aka zabe shi shugaban kasa gwamnatin sa zata kirkiro da zuba kaudi a cikin tattalin arzikin kasa yadda yan kasuwa baza su din dogaro akan bashin bankuna ba. Ya ce, kudin ruwan na banki ba zai wuci digo daya ba, ba kamar akshi 30 bisa dari na kudin ruwa. Acewar Farfesa Kingsley Moghalu, akwai dimbin talauci a kasar nan kuma akwai bukatar a samar da tsari don rage talaucin. Acewar Farfesa Kingsley Moghalu gwamnatin sa zata tabbbatar da ta samar da tsare-tsare don dakile satar fasaha harda ta rubuce-rubucen litattafai da ta kade-kade da daukacin fadin kasar nan. Ya kara da cewa, gwamnatin sa in har a zabe shi, za ta tabbatar da ta bunkasa fannin kirkire-kirkire, musamman don kara ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba a karni na 21. A karshe ya ce, za’a samu cin nasara hakan ne ta hanyar samo masu zuba jari.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!