Connect with us

SIYASA

Mun Gamsu Da Hukuncin Kotun Abuja A Kan Kujerar Sanatan Neja ta Gabas – Wana

Published

on

Babban Kotun Tarayya mai mazauni a Abuja ta tabbatar Alhaji Sani Musa 313 a matsayin dan takarar kujerar sanata mai wakiltar Neja ta gabas, mai makon Sanata Dabid Umaru da jam’iyyar APC ta sanar tun da farko. Hukuncin babban kotun ya ta’allaka ne da sakamakon zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a watan Oktoban shekarar da ta gabata, inda Alhaji Sani Musa 313 ya samu kuri’u 39,192 ya yin da sanatan wanda ke kai Sanata Dabid Umaru ya samu kuri’u 5,870.
Hukuncin kotun wanda ya yi fatali da matakin uwar jam’iyyar APC ta kasa, na kakaba ‘yan takara sabanin wanda jama’a suka zaba, ya nuna kuskure ne jam’iyyun siyasa su cigaba irin wannan karfa-karfa wanda ya sabawa kudin tsarin jam’iyyar tun farko. Duk wani matakin da ya sabawa kudin dokokin jam’iyya da kuma tsarin dokokin zabe tamkar karan tsaye ne wa dokokin kasa.
Alhaji Muhammad Awaisu Wana, jigo a jam’iyyar APC a jihar Neja, yace wannan hukuncin na kotu ya yi dai-dai domin hakan ne kawai zai iya kawo karshen kakabawa ‘yan takarar da jama’a ba su so da jam’iyyun siyasa ke yi. Sanin kowa ne an yi zaben fidda gwani a jihar Neja mai makon a bar jama’a da zabinsu sai aka kasa yin hakan, Alhaji Sani Musa 313 na da kuri’a sama da dubu 39 amma sai uwar jam’iyya ta kasa taki amincewa da zabin jama’ar Neja ta gabas, jama’a ne suka zabi Barista Dabid Umaru a 2015 a matsayin sanata, aka ki ba shi zaben sa bayan ya tafi kotu ya samu nasarar karban kayansa, to bai wa jama’ar aikin komi da ya tafi majalisar ba, sai a zaben fidda gwani jama’a suka juya ma shi baya suna bukatar canji, to in ko haka ne ya zama wajibi ‘yan siyasa su san cewar in an zabe su ba wai an tura su ba ne dan zaman dumama benci ba, domin akwai ranar kin dillanci kamar yadda ya faru da shi Barista Dabid Umaru a yanzu.
Irin wannan matakin na kotu da sauran alkalai zasu rika tsayin daka wajen yin aiki wa kasa tsakanin su da Allah da zarge-zargen da ake masu na rashin gaskiya da ya kau, jam’iyyar APC a matakin kasa bisa jagorancin Adams Oshimole tayi abinda ta ke so, maigirma shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya umurci duk wanda aka tauye ya je kotu kuma mun fara ganin alkiblar shugaban kasa akan shugabanci na gaskiya da adalci, wanda hakan yasa yake kara samun tagomashi da karbuwa a wajen talakawan kasa. Ina jawo hankalin shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshimole da ya koma kan turbar da aka san shi da ita na gaskiya kimarsa da darajar sa za ta sake dawo wa, domin dimukuradiyya ake yi kuma shi ma Adams din ya ci ribar kotu a baya wanda ta ba shi damar zama gwamna na tsawon shekaru takwas a jihar Edo.
Wana ya jawo hankalin magoya bayan Sanata Dabid Umaru da su kau da bambamce bambamcen siyasa a tsaya a yiwa jam’iyyar APC aiki, domin muna da babban zabe a gaban mu ita siyasa wasa ce, in ka zama mai biyayya kana zaune wata rana sai ka ga rabon ka ya same ka, kar mu bari a raba kan mu da maganar addini, domin jam’iyya ce ta hada mu ba yare ko addini ba, duk wanda ya kitsa maku wata tsana ta harshe ko addini ba masoyin kasar nan ba ne domin dukkan mu daya ne kuma jam’iyya daya ce ta hada mu sai mu fuskanci mataki na gaba dan kai kasar nan ga tudun natsira.
Ina jawo hankalin alkalan kasar nan da su ji tsoron Allah su rika kwatanta adalci a shari’o’in da ke gabansu kasar za ta cigaba kuma jama’a zasu zauna lafiya, kamar Sanata Dabid Umaru yaci anfani kotu a baya, haka yanzu ma da wannan canjin Alhaji Sani Musa 313 zai anfana da hukuncin kotu bisa zabin al’umma ka ga ke nan dimukuradiyyar ta fara zama da gindinta domin matakai uku ne suka haifar da shugabancin, wanda kotu na sahun gaba, kuma wannan matakin a matsayin mu na ‘yan siyasa masu son cigaban dimukuradiyya yayi muna daidai domin wannan shi ne bukatar jama’a, saura da me shi kansa Sanata Dabid Umaru ya rungumi hukuncin kotun dan a samu tafiya mataki na gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: