Connect with us

LABARAI

NBC Ta Kammala Shirin Samar Da Kwalabe Masu Inganci

Published

on

Kamfanin NBC ya sanar da cewar, yana shirin kammala sarrafa kwalabe masu ingancida aka fara gudanarwa a shekarar 2008 tare da kuma inganta ayyukan sa a cikin wannanan shekarar. Manajin Daraktan kamfanin Mista George Polymenakos ne ya sanar da hakan, Inda ya ce, munyi amanna cewar, kasuwancin my zai kara yin karfi ne a yankunan da muke gudanarwa, inda ya ce, misaliba cikin wannan shekarar nun kammala aikin mu na yin amfani da sababbin kwalaben da za’a dinga yin amfani dash a daukacin fadin kasar nan. Ya ce, shekaru goma da suka wuce aka fara gudanar da aikin na samar da sababbin kwalaben wanda yana daya data cikin kokarin da kamfanin take yi don tsaftace muhalli. Manajin Daraktan kamfanin Mista George Polymenakos ya ci gaba da cewa, hakan zai kara samarwa da kamfanin zuba jarin da ya kai na samada na euro miliyan 500 da za’a amfana kai tsaye a cikin shekaru hudu. Sai dai, Manajin Daraktan kamfanin Mista George Polymenakos ya yi nuni da cewar, tattalin arzikin kasar nan yana yin tafiyar Hawainiya amma duk da hakan, kamfanin yanada yakinin samun fadadar kasuwancin sa a cikin wannan shekarar ganin cewar an dora shi akan turba lr data dace, musamman ta hanyar samar da ingantattun kayan aiki. Ya ce, kamfanin ya kara inganta ayyukan sa da kuma samar da shirin da ya fara aiki tun a shekarar 2015, Inda hakan ya kara bashi kwarin gwaiwar samun zuba jari na sama da euro miliyan 500 da kuma fadada wajen sarrafa kayan sa dake a yankin Asejire a anguwar Ikeja, Abuja, Owerri, Challawa, Maiduguri, Fatakwal da kuma garin Benin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!