Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

NDLEA Ta Cafke Mutum 64 Da Laifin Safarar Kwayoyi A Jihar Jigawa

Published

on

Hukumar hana sha da kuma fataucin mugayen kwayoyi ta kasa ta fara farautar masu tu’ammali da hakan ko ina suke cikin jihar, Kwamandar ta jihar Jigawa Josephine Obi, ita ce wadda ta bayyana hakan a Dutse ranar Asabar.
Obi ta bayyana cewar ana ci gaba da kai samame wadanda ma’aikatan suke yi, a wurare daban- daban, a dukkanin kananan Hukumomi 27 na jihar.
Ta ci gaba da bayanimn cewar su ayyukan na samamaen da ake yi yanzu, ana yin su ne, sabopda a kauce ma samun matsaloli lokacin zabubbukan 2019.
“Kamar dai yadda ta ci gaba da bayanin cewar Hukumar ta NDLEA reshen jihar Jigawa ta kara sa kaimi, wajenn ffutukr kokarin da take yi na, yaki da masu hada-hadar muggan kayoyi, abode ayi maganin aikata laifuka da kuma tashe-tashen hankula yayinn da ake kara kusa da zabubbukan shekara ta 2019.
“Munayin hakan ne ta hanyar wayar da kan al’umma, kara bincike -bincike da kuam zurga zurga, da kuma a fasa duk wuraren da ake sayar da muggan kwayoyi, da suke illahirin jihar Jigawa..
“An dai fara yin shi wannan kai farmakin tuna tan Janairu, kuma zuwa yanzu kuma an samu nasara saboda an samu lalata wurare masu yawa, an kuma mutane 64 wadanda suka hada da mata sai kuma kilogiram17.55 na mugayen magunguna, daban – daban.
Har ila yau kamar yadda ta kara bayyanan su kayayyaykin magungunan da suka kwace sun hada da Cannabis Satiba, Tramadol, Edol, Dapsol, Diazepam, Codeine, Rubber Solution and Formalin,wanda kuma aka fi sani da Suck and Die.
Sai dai kuma duk hakan Obi har ila yau daga cikin mutane 61, wadanda kuma bayan da aka, gwada su an gano cewar suna mafani da mugayen kwayoyi, bayan nan kuma an ja masu kunne aka kuma sallame su, wadanda kuma su diloli ne su za’a tura su ne zuwa kotu.
“Saboda haka muna kira da kowa domin ya rika lura da al’amura musamman wadanda suka shafi tsaro, bama kamar irin asu tarurrukan da ake yi wadanda basu dace ba. Ana ma iya la’akari da wuararen da ake sayara da magunguna, komai na iya fauwa a ire-iren su wuraren. Hara yanzu dai kamar yadda ta kara bayyanawa shi wannan sintirin musamman ana ci gaba da yin shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: