Connect with us

WASANNI

PSG Abin Tsoro Ne Idan Suna Buga Wasa A Gida, In Ji Solkjaer

Published

on

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya ce ‘yan wasansa zasu iya shan wahala sosai a zagaye na biyu na wasan da zasu yi tattaki zuwa kasar Faransa don karawa da kungiyar PSG, a gasar zakarun turai mataki na kungiyoyi 16 a ranar 3 ga watan gobe
A zagayen farko na wasan dai Manchester United ce zata karbi bakuncin PSG a wasan da zasu fafata a filin wasa na Old Trafford dake kasar Ingila wasan da kuma dan wasa Cabani shima watakila bazai samu damar bugawa ba.
Tuni dai aka tabbatar da cewa dan wasa Neymar bazai samu damar buga wasan ba sakamakon ciwo dayaji a kafarsa kuma hakan yasa kungiyar ta hakura da dan wasan wanda ake ganin babu kamarsa a kungiyar.
Solkjaer dai ya yi gargadin cewa dole Manchester United ta jajirce a wasa na biyu da zata yi tattaki zuwa Faransa, ba tare da la’akari da rashin babban dan wasan kungiyar ba wato Neymar, dan kasar Brazil.
Tun a farkon kakar wasa ta bana Manchester United ke fuskantar kalubalen koma baya kan nasarorin da ta saba samu a wasanninta, musamman a lokacin tsohon kociyan kungiyar Jose Mourinho.
Kalaman na Solkjaer sun zo ne a dai dai lokacin da shi ma, dan wasan gaba na kungiyar PSG, Cabani, ya jadadda cewa kungiyar tasa, zata iya kai wa ga zagaye na gaba a gasar zakarun turan, duk da cewa babu tabbas din idan zaiyi wasan farko na gobe.
Ko da yake Cabani ya ce wasan zagaye na biyu da zasu fafata a ranar 3 ga watan Maris mai wahala ne, yana da kwarin gwiwar zasu iya samun nasara akan yaran Solkjaer duk da cewa basu san yadda sakamakon gobe zai kasance ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!