Connect with us

WASANNI

Real Madrid Za Ta Kamo Barcelona

Published

on

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Santiago Solari, ya bayyana cewa kungiyarsa zata iya kamo wadda take mataki na farko akan teburin na laliga wato Barcelona idan har suka cigaba da samun nasara.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta dawo matsayi na biyu a gasar Laliga a ranar Asabar din data gabata bayan tasamu nasara akan abokiyar hamayyarta ta Atletico Madrid a wasan hamayyar da suka fafata.
Sun dawo na biyunne bayan sun casa abokanan hamayyarsu na cikin gida wato Athletico Madrid inda suka yimusu ruwan kwallaye 3-1 bayan sunsha gumurzu kuma ‘yan wasa Casemiro da Ramos da Bale ne suka zurawa Real Madrid kwallo a raga.
Sakamakon wannan rashin nasara da Atletico Madrid din sukayi ya sa sun koma matsayi na 3 hakan yana nufin Barcelona zasu sami matsin lamba duba da cewa yanzu Real Madrid ne suke binsu a baya?
A kwanakin baya kociyan Barcelona, Enesto Valverde ya ce za su wuce su dauki Laliga sumul kalau batare da wata fargabar Real Madrid na binsu a baya ba matakin da a yanzu ake ganin kamar abune mai wahala.
Dan wasa Gareth Bale, wanda ya zura kwallo ta uku a wasan ya zura kwallonsa ta 100 a Real Madrid tun bayan daya koma kungiyar daga kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a shekara ta 2013 akan kudi fam miliyan 83.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!