Connect with us

LABARAI

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Yi Sabon Kakaki  

Published

on

Rundunar sojin Nijeriya ta nada Kanal Sagir Musa., a matsayin jami’in hulda da jama’a na rundunar, Sagir din ya maye gurbin Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ne, wanda ya yi ritaya a cikin makon da ya gabata, nadin Sagir din yana da cikin sabbin nade-nade da rundunar ta yi wa wasu manyan jami’anta a cikin makon da ya gabata.

Kafin wannan sabon mukamin, Sagir Musa shine kakakin rundunar sojin ta 82 da ke garin Inugu, an maye gurbinsa da Kanal A.A Musa a matsayin jami’in hulda da jama’a na rundunar 82 dake garin Inugu, a yayin da aka tura Kanal A.D Isa a matsayin jami’in hulda da jama’a na rundunar atisayen Lafiya Dole, shi kuma Kanal Onyema Nwachukwu an mayar da shi ma’aikatar tsaro dake Abuja.

Rundunar ta yi manyan sauye-sauye da canje-canjen wajen aiki ga manyan jami’anta, inda da yawansu aka canja musu guraren da suke aiki zuwa wasu sabbin wuraren na daban.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!