Connect with us

KASASHEN WAJE

Shirin Rigakafin Cutar Ebola Ya Samu Gagarumar Nasara

Published

on

Ma’aikatar Lafiyar Jamhuriyar Congo, ta ce mutane 502 sun rasa rayukansu, tun bayan sake bullar cutar Ebola a kasar cikin watan Agustan bara.
Sai dai yayin da yake kain bayani kan halin da kasar ke ciki dangane da bullar cutar, Ministan Lafiya, Ilunga Kalenga, ya ce a karon farko shirin gwamnati da hadin gwiwar hukumomin lafiya na duniya wajen yiwa al’ummar kasar rigakafi, ya samu nasarar kare mutane dubu 76, da 425 daga kamuwa da cutar.
A watan Agustan bara Ebola tasake bulla a arewacin yankin Kibu, da ya yi iyaka da kasashen Uganda da Rwanda, karo na 10 kenan kuma cutar na bulla a Jamhuriyar Congo, tun bayan soma gano ta a kasar cikin shekarar 1976.
Hukumar lafiyata duniya WHO, ta ce barkewar cutar a baya bayan nan, da ke haddasa zubda jinni ta kafofin jiki, bayaga zazzabi mai zafin gaske, ita ce annoba ta biyu mafi girma, bayan bullar cutar a kasasshen Saliyo da Liberia a shekarun bayan, inda ta hallaka sama da mutane dubu 11,000.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: