Connect with us

MANYAN LABARAI

Sojin Chadi Sun Yi Gagarumar Nasara Kan ‘Yan Tawaye

Published

on

Ma’aikatar tsaron Chadi ta tabbatar da kame ‘yan tawaye fiye da 250 ciki har da jagororinsu bayan wani sumame da ta kai kan ayarin motocinsu lokacin da su ke shirin tsallako iyakar kasar daga Libiya cikin watan Janairu.
A sanarwar da Babban hafson sojin kasar ya fitar a yau, ya ce za su ci gaba da kai sumame maboyar ‘yan tawayen yankin Ennedi da ke gab da kan iyakar kasar da Libya da Sudan baya ga sanya tsaurarn matakan tsaro.
Sanarwar ta ce mayakan ‘yan tawayen su 250 tare da jagororinsu 4 yanzu haka na hannun hukuma yayin da aka lalata motocinsu fiye da 40 a hare-haren ciki har da wadanda aka kai ta sama da jiragen yakin Faransa.
A makon jiya ma shugaban kasar Idris Deby ya sanar da cewa dakarun sojin kasar sun yi gagarumar nasara kan ‘yan tawayen da ke kaddamar da hare-hare a kasar.
Chadi wadda ke cikin kasashen G5 Sahel da ke fuskantar hare-haren ta’addanci ko a bara ta fuskanci hare-haren ‘yan tawayen matakin da ya tilasta mata daura damarar yakarsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: