Connect with us

KASASHEN WAJE

Tattalin Arzikin Duniya Na Fuskantar Babban Barazana –IMF

Published

on

Asusun bada lamuni na duniya wato IMF ya gargadi gwamnatocin kasashe game da barazanar da ke tunkaro tattalin arzikin duniya a shekararnan, inda ta ce babu tabbacin za a fuskanci habakar tattalin arziki a bana.

 

A jawaban da ta gabatar, Babbar manajar Asusun ta IMF Christine Lagarde ta ce tafiyar hawainiyar da habakar tattalin arziki ke yi a watannin nan manuniya ce ga kalubalen da duniya za ta fuskanta ta fuskar tattalin arziki a bana.

 

Yayin taron tattalin arzikin da ya gudana a birnin Dubai na hadaddiyar Daular larabawa, taron da ya samu halartar wasu shugabannin na duniya.

Christine Lagarde ta alakanta batutuwa masu alaka da rikicin kasuwancin karin haraji kan kayayyaki tsakanin kasashe da rashin tabbas kan ficewar Birtaniya daga EU da kuma tsuke bakin aljihu a matsayin dalilan durkushewar tattalin arziki a bana.

 

Ko a watan da ya gabata, IMF ta sassauto da hasashenta na bunkasar tattalin arziki a bana daga kashi 3.7 zuwa kashi 3.5 cikin dari.

 

A cewar Legarde rikicin kasuwancin da kuma mayar da martanin haraji tsakanin kasashen Amurka da Sin na ci gaba da tagayyara tattalin arzikin duniya, la’akari da matsayinsa na mafiya karfin tattalin arziki a kasuwancin duniya.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!