Connect with us

WASANNI

Tottenham Ma Za Ta Iya Lashe Gasar Firimiya

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Maurucio Pochettino ya bayyana cewa sakamakon irin nasarar da kungiyarsa take samu da kuma yadda kungiyoyin da suke saman teburi suke rasa maki zasu iya lashe gasar ta bana
Tottenham ta yi nasarar doke kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, wato tsohuwar zakara a gasar da ci 3-1 a wasan mako na 26 a gasar cin kofin firimiya da suka fafata a ranar Lahadi a filin wasa na Wembley.
Tottenham ta fara cin kwallo ne ta hannun dan wasan baya Dabinson Sanchez a minti na 33 da fara wasa, Leicester ta samu damar farkewa a bugun fenariti, amma Jamy Bardy ya barar da fanaretin.
Bayan da aka koma daga hutu ne Eriksen ya kara kwallo ta biyu daga baya Bardy na Leicester ya zare kwallo daya, sai dai daf da za a tashi daga fafatawar Son Heung-Mi ya ci ta uku kuma aka tashi wasa.
“Muma yanzu muna cikin lissafin kungiyoyin da zasu iya lashe wannan gasa saboda muna samun nasara akai akai kuma su kungiyoyin da suke saman teburin sun aasarar maki” in ji kociyan kungiyar, dan asalin kasar Argentina
Yaci gaba da cewa “ Duk da cewa munada manyan ‘yan wasanmu wadanda basa buga wasa saboda ciwo irinsu Harry Kane da Delle Alli amma a haka muke dagewa tabbas idan suka dawo zamu kara karfi”
Da wannan sakamakon Tottenham tana nan a mataki na uku da maki 60, maki biyar tsakaninta da Liberpool ta biyu a teburi, sannan maki biyar itama tsakaninta da Manchester City wadda ta doke Chelsea.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!