Connect with us

KASASHEN WAJE

Turkiyya Ta Bukaci Sin Ta Rufe Sansanin Azabtar Da Musulmin ‘Yan Kabilar Uighur

Published

on

Kasar Turkiyya ta bukaci kasar Sin da ta rufe sansanonin da ta ke tsare da mabiya addinin Musulunci daga kabilar Uighur sakamakon mutuwar wani fitaccen mawaki mai suna Abdurehim Heyit.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Turkiyyar ta fitar ta nuna cewa; mawakin da aka daure shekaru 8 a gidan yari ya mutu sakamakon azabtarwar da ake musu a sansanin.

Su dai ‘yan kabilar Uighur, tsiraru ne kuma Musulmai ne a kasar ta Sin wadanda ke zaune a yankin Xinjiang, kuma harshensu ya so ya yi kama da na Turkiyya.

Sai dai kasar ta Sin din ta bayyana bukatar Turkiyyar a matsayin abin da ba zata amince da shi ba.

Ko a baya-bayan nan dai daruruwan ‘yan Kabilar ta Uighur sun yi ta yin hijira zuwa Turkiyya don samun saukin rayuwa daga azabtarwar da su ke fuskanta can a Sin.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!