Connect with us

LABARAI

‘Yan Achaba Sun Gwabza Da ‘Yan Sanda A Abuja

Published

on

A ranar Asabar ne wasu ‘yan acaba suka gwabza da ‘yan sanda a garin Kubwa da ke cikin Abuja. Wadanda lamarin ya auku a gaban idanunsu sun bayyana cewa, lamarin ya auku ne da misalin karfe 2 na rana kusa da gidan mai Total Filling Station, a mahadan 2.2, lokacin da ‘yan sanda suka zargi ‘yan acaban a kan gudanar da aiki ba bisa ka’ida ba, ina suka yi amfani da bindiga wajen dukan wani dan acaba.
A cewar wani wanda lamarin ya auku a gaban idanunsa mai suna Mista Daniel Ibe ya yi kuka a kan raunin da suka ji wa abokinsa dan acaba wanda ya tsaya kusa da inda lamarin ya auku, nan take aka gudanar da zanga-zanga. “’Yan sanda suna ta dukan dan acaban da sanda saboda yaki tsayawa a wajen da suke tsayawa, inda suka karya masa kashi,” in ji shi.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ta ruwaito cewa, yawancin ‘yan acaban sun killace hanyar Gado Nasko, inda ya janyo cinkosan ababan hawa a kunguwan. ‘Yan acaban sun fara saka wuta a yanyar, inda ya tilasta wa masu motoci tsyawa. An girke jami’an ‘yan sanda a kan hanyar inda suke ta harbi sama domin tarwatsa ‘yan acaban, amma duk da haka bai sa sun tarwatse ba. Hankula ya kwanta ne lokacin da DPO da ke kula da Kubwa ya roki ‘yan acaban. DPO ya gayyaci ‘yan acaban zuwa ofishinsa domi tattaunawa, wannan shi ya kawo karshan rikicin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: