Connect with us

WASANNI

Yanzu Kuma Matsayi Na Uku Muke Hari – Solkjaer

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer ya bayyana cewa kawo yanzu kuma yana neman matsayi na hudu ne a gasar firimiya bayan da kungiyarsa ta fara dandana matsayi na hudu a karon farko tun farkon fara wannan gasar.
Likkafar Manchester United na ci gaba da dagawa a gasar firimiya ta Ingila, bayan da kungiyar ta lallasa takwararta ta Fulham da kwallaye 3-0 a ranar Asabar din data gabata a wasan sati na 26 na gasar firimiya.
Nasarar ta bai wa Manchester United damar komawa mataki na 4 a gasar ta firimiya daga matsayi na 6 da ta ke kai a baya a lokacin tsohon kociyan kungiyar, Jose Mourinho wanda kungiyar ta sallama a watan Disambar daya gabata.
‘Yan wasan Manchester United Paul Pogba da Martial ne suka jefa kwallayen a ragar Fulham kuma karo na farko kenan da Manchester United ta samu nasara a jimillar wasanni 6 da ta fafata a gidan abokan karawarta, tun bayan irin bajintar da ta nuna a kakar wasa ta 2009 cikin watan Mayu.
Tun bayan karbar ragamar jagorancin Manchester United da Ole Gunnar Solskjaer ya yi daga hannun Jose Mourinho, kungiyar ta samu nasara a wasanni 10, daga cikin jimillar wasanni 11 da ta fafata.
Ranar Talata 12 ga watan Fabarairu wato gobe, PSG za ta yi tattaki zuwa Ingila, domin fafata wasan zagayen farko tsakaninta da kungiyar Manchester United, a gasar zakaru nahiyar Turai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!