Connect with us

MANYAN LABARAI

Yarjejeniyar Zaman Lafiya: Buhari Da Atiku Za Su Rattaba Hannu A Gaban Clinton

Published

on

Shugaban Amurka na 42, Bill Clinton da Sakatare Janar na kungiyar kasashe renon Birtaniya, Baroness Patricia Scotland, na daga cikin manyan bakin da ake sa ran za su harlaci taron sa hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a taron tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ‘yan takaran shugabancin kasar nan.
An shirya gabatar da taron ne a babban dakin taro na ‘International Conference Centre’ dake Abuja a ranar Laraba 13 ga watan Fabrairu.
Masu shirya taron na zaman lafiya sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasar nan Amurka zai yi ganawa na musamman da dan takarar shugabanci kasa na jam’iyyar APC kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarare shugabacin kasar na a karkkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
“A daidai lokacin da muke shiga harkokin zabe a kasar nan dole mu dauki duk wani barazana ga zaman lafiya da mahimmancin gaske”, inji kungiyar ta NPC.
Samarwa da ta fito daga babbar Sakatarin kungiyar na zaman lafiya, ‘National Peace Committee’ mai suna ‘The Kukah Centre’, Fr. Atta Barkindo, ya ce, an shirya sa hannun ne da nufin duk masu ruwa da tsaki a harka zaben za su rungumi dukkan sakamakon zaben da hukumar zabe ta INEC za ta sanar ba tare da wani nukura ba.
Barkindo ya kuma kara da cewa, “Kwamitin zaman lafiya a bukatar ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali tare kuma da mika mulki ga jam’iyyar da ta ci zabe a yayin aka sanar da wanda ya ci zaben gaba daya.
“A kan hake ne, muka gayyaci Shugaba Bill Clinton, shugaban kasar Amurka na 42 da Baroness Patricia Scotland, Sakatare Janar na kungiyar kasashe renon Birtaniya, zuwa Nijeriya daga ranar 12 zuwa 13 ga watan Fabrairu 2019, gab da fara zaben shugaban kasa a Nijeriya, an shirya za su gabatar da jawabin ga malaarta taron a ranar 13 ga watan Fabrairu,” inji sanarwar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!