Connect with us

KASUWANCI

Za A Samar Wa Kamfaninin Gine-Gine Bashi Mai Saukin Ruwa

Published

on

A ranar Alhamis data wuce Gwamanatin Tarayya ta bayyana cewar, zata samar da rance ga kamfannonin masu gina gidaje a kasar nan wanda baida wani ruwa don ginawa ma’aitan gwamnati gidaje.Shugabar ma’aikata ta tarayya uwargida Winifred Oyo-Ita ce ta bayyana hakan a garin Abuja a loacin da take bayyana kokarin da ofishin ta ya yi a cikin shekaru uku da suka gabata. Winifred Oyo-Ita ta ce, kokarin amn mayar da hankali ne wajen yiwa aikin na gwamnati garanbawul a cikin shekaru uku da suka gabata don a tabbatar da ana bin ka’ida da kuma inganta ayyukan na gwamnatin tarayya. Acewar ta, an tura wasu jami’an gwamnatin tarayya zuwa kasar Rwanda don koyo harkar gudanar da mulki da kuma koyon darasi akan yadda kasar ta fuskanci mummunan yaki a shekaru da dama da suka shige. Ta kara da cewa, ma’aikatan gwamnati su 10,735 aka yiwa karin girma duk a cikin shekaru ukun da suka shige, an kuma canzawa ma’aikatan su 872 wajen aiki, inda kuma ma’aikatan su 4,527 suke jiran sakamakon su na karin girma na jarrabar shekarar 2018. Oyo-Ita ta ci gaba da cewa, tuni ma’aikatan sama da 8,000 suka amfana da shirin gidaje na gwamnatin tarayya don kara inganta walwalaer su. Acewar uwargida Winifred Oyo-Ita ofishin ta ta taka rawa wajen amincewa da sabon albashi mafi karanci na ma’aikata da ya kai naira 30,000. Ta ce, gwamnatin tarayya tana kan tattaunawa akan bashin gina gidajen da gidauniyar Family Homes don kara gina gidajen da basu da kudin ruwa.Ta sanar a karkashin shirin na FISH za’a samar da ingantattun gidaje ga ma’aikatan, inda a yanzu ake kan gina gidaje har guda 9,503, inda kuma tuni aka rabar da gidaje guda 342. Acewar ta,jimlar ma’aikata su 4,167 suka amfana a karkashin shirin na FGSHL da gwamnatin ta yi hadaka da bankin tarayyya dake bayar da bashin gina gidaje.A karshe uwargida Winifred Oyo-Ita ta bayyana cewar, ma’aikata har su 2,077 suka amfana da shirin bayar da bashi na gyran gidaje da ya kai naira miliyan daya wanda aka wanzar da shirin tare da yin hadin gwaiwa da bankin tarayyya dake bayar da bashin gina gidaje a shekara 2016 zuwa shekarar 2018.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: