Connect with us

MANYAN LABARAI

Zabe: Hukumar DSS Ba Za Ta Lamunci Labaran Bogi Da Kalaman Batanci Ba –Kakakin Hukumar

Published

on

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta yi wani gargadin ga masu yada labaran bogi, da kuma masu furta kalaman batanci wadanda ka iya harzuka al’ummar su haifar da fadace-fadace na kabilanci, addini ko kuma na siyasa musamman a lokutan zabe, hukumar tayi wannan gargadin ne a daida lokacin da muke fuskantar zabukkan shekarar 2019.

Kakakin hukumar, Mista Peter Afunanya ne ya yi wannan gargadin yau Litinin a babban ofishin hukumar dake garin Abuja, ya shawarci masu wannan dabi’un da su taimaki kansu su daina tuin wuri, saboda haka yana iya haifar wa da kasar nan mummunan tashin hankalin da Allahn kadai yasan illar da zai haifar.

‘Hukumar mu ba zata zauna ta zuba ido ba, a daidai lokacin da bata gari suke neman jifa kasar nan cikin halin kaka-ni-kayi, don haka dole mu yi wannan gargadin, sannan muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su tabbatar da sun kiyaye dokokin kasa, sannan su kasance masu kiyaye zaman lafiya.’ Inji Afunanya

Kakakin ya shawarci ‘yan siyasa da matasa su kiyaye tayar da hankulan al’umma, da dukkan wani abu da zai iya haifar da tashin-tashina a lokutan zabe, saboda hukumar su ta shirya tsaf don kamewa da hukunta duk wani da ya tada hankulan al’umma a lokutan zabukka.

Afunanya ya kara da cewa; hukumar DSS ta tabbatar da za ta yi amfani da hurumin da dokar kasa ta tanadar mata, wajen gano dukkan wata barazana da ke iya fuskantar kasar nan, sannan zata yi aikin gano dukkan wani bata gari da gurfanar da shi a gaban doka don fuskantar hukuncin da ya dace.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: