Connect with us

LABARAI

Zaben 2019 Na Fuskantar Barazana –Buhari

Published

on

Shugaba Buhari ya koka a kan yanda babban zaben 2019 yake fuskantar barazana sabili da matsalar cin hanci da rashawa.
Cikin wata makala ta shugaban kasan mai taken, “corruption threatens Nigeria – and its election” ( Cin hanci da rashawa yana barazana ga Nijeriya, da zaben ta), yana cewa, cin hancin da rashawa yana yi wa babban zaben shugaban kasa na ranar Asabar har ma da tsarin Dimokuradiyya barazana.
“A matsayina na Shugaban kasa, na yi iya iyawa na wajen tsare gaskiya a kan aikin da aka dora mani na ganin na hana cin hanci da rashawa, samar da tsaro, da farfado da tattalin arziki. Duk suna da mahimmanci. Amma dayansu duk ya fi su mahimmanci, shi ne kuwa kawar da cin hanci da rashawa.
“Duk wani tsarin da ba zai yaki cin hanci da rashawa daga tushen sa ba, tabbas wannan tsarin zai ruguje ne. yaki da cin hanci da rashawa shi ne ya kamata ya zama tushen gyara kasarmu, gina tattalin arzikinmu, samar da kyawawan manyan ayyukan raya kasa da ilmantar da zuriyarmu.
“Wannan shi ne kalubalen da ke gabanmu: wanda ya kamata mu dora nasarar kasarmu a kansa. Amma abin da ke faruwa a halin yanzun zai iya sanyawa wannan yakin ya zama mai wahala. Ina nufin yanda ake satar dukiyar kasa, shi kanshi cin hanci da rashawan da karfinsa yake tafiya. Za kuma su yi amfani da shi. A duk lokacin da kake yakar cin hanci da rashawa, ka tabbatar da shi ma zai yake ka.
“Yana ma barazanar kaskantar da zaben watan Fabrairu, har ma da tsarinmu na Dimokuradiyya. Hukumar EFCC ta ankarar a kan yanda ake ta amfani da kudi wajen siyan kuri’u.
Buhari ya ce, wadanda suke sukan gwamnatinsa a kan yakin da take yi da cin hanci da rashawa sune masu sukar tsarin na shi.
“Duk da cewa Lauyoyin su za su iya yin jayyaya sosai, amma ba za su iya gujewa abin da ya hada su wuri guda ba: mahimman takardun shaida na shari’a a sarari, kamar ko takardun Panama, rahoton Majalisar Amurka, bayanan kamfanin mai na Shell ko asusun ajiya na bankuna.
“Amma a lokacin da muke karfafa yakar cin hanci da rashawa, sai muka ga cin hancin da rashawa yana kokarin ya fi karfin doka.
“Da zaran mun kyale su, kamar yanda suke a can baya, kwadayin wadanda ake hada kai da su zai karu ne. Mun rigaya mun dunkule su waje guda, amma abin takaicin shi ne har yanzun akwai wasu daidaiku da a shirye suke da su bude masu taga,” in ji shi.
Shugaban ya ce, “Duk da cewa an samu ci gaba sosai a kan hakan, amma har yanzun akwai sauran aiki a gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!