Connect with us

LABARAI

A. A. Zaura Ya Jaddada Aniyarsa Ta Kauda Shan Maye A Tsakanin Matasa

Published

on

Dan takarar Gwamnan jihar Kano a inuwar jam’iyyar GPN. Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura ya jaddada aniyarsa ta kauda matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa a jihar Kano ta samar musu da sana’oi na dogaro dakai da rashin sana’ar ke taimakawa sosai wajen kara ta’azzara lamarin da ake sanya Kano akan gaba wajen ta,ammali da kayan maye.
A.A.Zaura wanda ya bayyana hakan a wajen yaye matasa guda 250 da wata kungiya ta wayarda kan matasan Fagge da suke goyon bayan takarsa daya dauki nauyin horas dasu a fannonin sana’oi daban-daban da aka gudanar a dakin taro na cibiyar nazarin damakwaradiyya dake Gidan Malam Aminu Kano da akafi sani da Gidan Mambayya yayi nuni da cewa idan ya zama Gwamnan Kano akwai tsare-tsare dazai kawo na kauda shan-kwaya a tsakanin matasan ta kawo wani sanadari da digon daya idan aka baiwa duk wani mai shan kayan maye zai daina,sannan a tarbiyantar dashi a bashi sana,a.
Dan takara ya yabawa kungiyar matasan na Fagge bisa tunaninda sukazo masa dashi mai kyau mai anfani ga al’umma wanda hakan tasa ya dauki nauyin sawa a horasda matasan akan koyon wadannan sana’oi na hannu da suka hada da yin jaka takalma da dinki wanda irin wadannan sana’io dasu kasashen duniya suka cigaba ake zuwa a sayo kayansu a kawo kasarnan.
Yace zai cigaba da hada hannu da kungiya ta Fagge Youths Mobilisation domin a cigaba da horasda matasa dake kananan hukumomi 44 na jiharnan tareda yin al’kawarin taimakawa wadanda suka anfana da horon da jari da zasu bunkasa sana’oi da suka koya.
A nasa jawabin dan takarar majalisar jihar na karamar hukumar Fagge karkashin jam’iyyar GPN. Abdullahi Yaron Mama ya bayyana farin cikinsa da kuma godewa A.A.Zaura bisa wannan abu daya dauki nauyi duba da cewa bai kai ga zama Gwamnan Kano ba yake irin wannan hidima ta son cigaban al’umma.
Danmama yace yanzu Zaura shi yake bin al’ummar Fagge bashi su fito su zabeshi da dukkan yan takarkari na majalisara tarayya dana jaha a karkashin jam’iyya su kuma tsare akwati dan tabbatarda an sami nasara.Yace a baya jam’iyyar APC sukeyi amma saboda irin karamci da kishin Dantakarar Gwamna na GPN ga cigaban al’umma suka koma GPN.A yayin taron an karrama dan takarar Gwamnan na jihar Kano da lambar yabo da kuma takardar shaida bisa irin gudummuwa da yake baiwa cigaban al’umma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!