Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

A Kan Satar Akuya A Bauchi ‘Yan Sintirin Da Ke Sun Kashe Mahauci

Published

on

‘Yan kungiyar sintiri na unguwa -unguwa wadanda kuama aka fi sani dfa suna ‘yan kamiti, ana zargiun su da zama sanadiyar mutuwar wani mutumi mahauci mai shekaru 28, wanda ake kira da suna Abdulrazak Hassan har lahira a sanadiyar gallazawar da suka yi ma shi daban- daban a Wuntin Dada cikin jihar Bauchi.
Majiya labarai ta Northern City News ta ruwaito cewar shi al’amarin ya faru ne ranar Jumma’a, wanda kuma shine yasa matasan da suke wurin suka harzuka, saboda hr ma sunyi barazanar cewar za su dauki fasaha, ajkan abin da ya faru, amma kuma sai manya suka hana su yin hakan.
Da yake yi ma manema labarai jawabi mahaifin marigayin Sarkin Pawa Wada, ya bayyana cewar ankama ani da Akuya, aka kuma kai shi ofishin ‘yan sintiri.
Wada ya kara jadadda cewar “ Shi Shugaban ‘Yan Kwamiti’, Mallam Abdulmumini Abbas ya tura yaran shi, su kamo dana, wanda shi a lokacin ya dukufa akan aikin shine ne, kawai saboda shi wanda ake zargin ya bayyana masu cewar ya san da na.
“Lokacin da suka kai shi ofishin, sun yi magana amma ni ban san irin maganar da suka yi ba, saboda ni ban bi su ba, amma na ji labarin cewar shi anda ake zargi da satar an sake shi daga baya, suka kuma kira mai Akuya suka damka ma shi ita.
“ Bayan dan lokaci kuma saiu suka kara taso da maganar sace rago, al’amarin da dana bai san wani abu ba, sai aka ce su , su biya dubu goma, wadancan kuma su bada dubu bakwai, To bayan sun tafi ne sai suka kashe mani da na, suka kuma dauke kudin shi, da kuma wayoyin shi.”
Mahaifin marigayin ya yi zargin cewar bayan sun kashe ma shi da wasu daga cikin ‘yan kungiyar sintirin, sai suka kawo gawar dan shi gida, amma kuma ai an gansu.
Y a ci gaba da bayanoin cewar lokacin daya dawo gida sai nana da nan ya tafi gidan mai garin Wuntin Dada ya shaida ma shi halin da ake ciki, shi mai garin ne ma, ya shaida ma jami’in ‘yansanda na GRA halin da ake ciki.
Wada ya kra bayyana cewar ‘yansanda su suka kai gawar dan shi zuwa asbiti, inbda kuma aka tabbatar da cewar ya rasu, daga nan kuma sai suka basu gawar saboda su yi ma shi jana’aiza.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: