Connect with us

LABARAI

Al’ummar Ibira Mazauna Kano Ta Bada Tallafi Ga Mutum 50

Published

on

Kngiyar al’ummar Ibira mazauna Kano da Jigawa ta bada tallafin jari ga ya’yan kungiyar dan gudanarda sana’oi dazai kawo cigabansu a yayin wani taro data gudanar a jihar Kano.Da yake jawabi a yayin taron Sarkin Ibira mazauna jihar Kano da Jigawa.Alhaji Ali Abdulmalijk yace an bada jarinne dan bukasa rayuwar wadanda suka anfana.
Sarkin na Ibira na jihar Kano Alhaji Ali yace duk inda al’umma Ibira take a Duniya mai son cigabane dan haka suna fata nan gaba suyi wani tallafin dayafi wannan dazai taimakawa bunkasar al’ummarsu da fannin cigaban rayuwa da dogaro dakai.Tareda yin kira ga wadanda suka anfana da cewa N10,000 ba karamin kudi bane da mutum zai iya sana’a ko shima a baya da jarinda bai wuce N6,500 ya fara sana’a ba har yakai inda yake na bunkasa.
Alhaji Ali Abdulmalik yayi anfani da wannan dama wajen jan hankalin al’ummar Ibira dama sauran al’umma na kasar nan akan muhimmancin fita yin zabuka a zabe mai zuwa da kuma zaben shugabanninda suka cancanta cikin lumana.
A nasa jawabin shugaba kungiyar al’ummar Ibira mazauna Kano Pharmacy Mahmud Odidi Ozige yace tasrin bada tallafin da sukayi ya mayarda hankaline ga fifita mata bisa la’akari da rauninsu da nauyinda ke rataye a wuyansu idan sukayi anfani da jarinda aka basu zai anfanesu da yardarm Allah kuma ta nuna musu yanda za suyi anfani dashi zai zame musu alhairi.
Pharmacy Mahmud Odidi yace an baiwa mata guda 40 da maza 10 kowanne an bashi N10,000 Duk kuma wadanda aka baiwa akwai sunansa da lambar wayarsa da unguwarda yake dana wanda ya kawoshi da zasu rika bibiya suga aga irin yanda yayi anfani dasu da cigabanda aka samu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!