Connect with us

KASUWANCI

An Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Daina Rage Farashin Man Fetur – Soyode

Published

on

Mai bai wa Shugaban Kamfanin rukunonin Dangote Shawara akan matatun mai da albarkatun sa Mista Babajide Soyode, ya shwarci Gwamnatin Tarayya ta daina yin ragin farashin mai samfarin PMS.
Soyode ya yi nuni da cewar, idan aka kammala aikin matar mai ta Dangote da kuma sauran kananan matatun mai a kasar nan, Nijeriya zata taimaka wajen hakar mai na kasan ruwa akan farashi dan kadan da kuma samar da daidaiton farashin albarkatun mai a daukacin nahiyar Afirka.
Soyode a cikin sanarwar da ya fitar a taron matatun mai, zirga-zirga da kuma albarkatun mai a taron mai na kasa da kasa na shekarar 2019 da aka gudanar a garin Abuja.
Ya jaddda bukatar Gwamnatin Tarayya data sanya ido yadda ya kamata a fannin hakar danyen mai da iskar gas na kasan ruwa a kasar nan.
Ya yi nuni da cewar, idan an kammala aikin matatar mai ta Dangote wadda ita ce mafi girma Nijeriya zata zamo mai dimbin mai da za’a dinga yin amfani dashi a cikin kasar nan da kuma wanda za’a dinga fitarwa zuwa kasuwannin kasashen duniya
. Ya kara da cewar, hakan zai kuma rage yadda ake shigowa da man da aka tace cikin kasar nan daga kasashen waje tare da kara daukaka darajar naira.
. Acewar Soyode, babu wata bukatar ci gaba da rage farashin sayar da man.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayyar ta cire tallafin da take baiwa man fetur ta kuma baiwa masana’antun masu zaman kansu damar kula da fannin hakar mai na kasan ruwa, inda ya ce, lurar bai wai za’a ci gaba da yinta bane har abada ba, domin dama can akwai wannan kular tun a shekaru 32 da suka shige, toh a nan, me kuma muke nema?
Ya kara da cewar, shin kasan iya adadin talakawan da suka amafana da da wadannan tsare-tsaren?
Acewar sa, ina ganin mutane ne ya kamata su bukaci a cire domin su abin girmamawa ne kuma bama bukatar gwamantin ta ci gaba da sanya idon akan abinda ya shafi farashin na mai, shin wanne irin ido suke iya sanyawa a fannin?
Ya yi nuni da cewar, babu wata kasa da ta ci nasara akan sanya farashi akan albarkatun ta na mai.
Soyode ya jadda da bukatar Kamfanin NNNPC ya gyra matatun mai na kasar nan yadda zasu dawo suci gaba da gudanar da aiki.
Ya sanar da cewar, matatar mai ta Dangote in an kammala ta, zata samar da gablngunan danyen mai guda 650,000 a kullum.
Matar man ta Dangote wadda tana daya daga cikin manyan matatun mai a duniya, kuma Nijeria ta kasance mai taka muhimmiyar rawa a fannin mai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: