Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Kama Matar Aure A Kan Cin Mutuncin ‘Yarta Saboda Ta Kasa Yin Kirga

Published

on

Wata matar aure mai suna Bisola ta ranta a na Kare saboda aikata laifin data yi nan a amfani da wata waya, ta bugi’yarta mai shekaru biyu, a sanadiya ta kasa karanta mata alkalumma, kamar yadda ya dace, yanzu dai an kama ta, domin jami’an farin kaya na Nigeria Security and Cibil Defence Corps, wadanda suke sashen ci gaban yara anda kum yake karkashin ma’aikatar harkokin mata da bunkasa jin dadin jama’a.
Jaridar PUNCH Metro ta bada bayanin cewar Bisola, lokacin da take koya ma yarinya kirga da misalin karfe takwas na dare ranar Talata, a gidan su wanda yake layin Danjuma, dakekaramar Hukumar Akure ta kudua jihar Ondo, wadda ake zargin ta bugi ‘yartata ne da rodi, lokacin data gane cewar yarinyar ba zata iya furta kirgar da ita mahaifiyar tata ke son tayi.
Majiyar tamu ta bayyana cewar kukan da yarinyar take yi ne, yasa makwabta suka yi zunbur suka shiga cikin gidan, saboda su ba ita mahaifiyar ta hakuri, amma kuma sai suka ga cewar ashe ma ita yarinyar ta ma ji wasu raunuka a jikin, saboda ai jini ya taru.
Wata makwabciyar su da ake kira da suna Tope Boyede wadda ita ce ba buga labarin abin da cikin shafin ta na sadarwa na Facebook ˆª ita ce ta buga labarin na cin mutuncin da aka yi ma ita yarinyar. Jaridar Punch Metro ta nuna rashin jin dadin ta akan matakin da Bisola ta dauka, inda tace, duk da yake ita yarinyar bata yin kamar yadda mahaifiyar tata take bukata, wannan bai bata damar tayi ma ‘yarta yadda taga dama ba.
Boyede ya yi bayanin cewar mahaifin ita yarinyar ya san cewar ita mahaifiyar ta kan bugi ita’yar tasu, ya ci gaba da bayanin cewar lokacin da jami’an masu kare yara daga ma’aikatar mata suka zo su kama matar tashi, amma sai suka samu ita Bisola ta gudu.
Sai shi mutumin ya ci gaba da bayanin “ Ni da mahaifiyar yarinyar muna zauna ne a gida daya, titin Danjuma, yadda muka san cewar ita yarinyar ta shiga cikin wannan halin shine, mahaifiyarta ta buge ta rodi sabod bata iya kirga ba, daga daya zuwa dari biyu (1-200), shi makwabcin anda dakin shi yake kusa dana mahaifiyar yarinyar, sai yaji tana yin Kuka.
“Makwabta sun yi kokarin su ceci yarinyar daga mahaifiyar, amma kuma abin da suka gani baya da kyau, saboda akai jin a jikin yarinyar. Da farko dai ita mahaifiyar tana koya ma ‘yar ta ne, ambata nambobi na kirga, amma kuma da yarinya ta kasa yin kamar yadda mahaifiyar take so, sai kawai ta fara bugun ta,da rodi. Yarinyar ko ma shekaru biyu cikakku bata yi ba, ko dai da yake mahaifiyar tana koya mata, amma don ta kasa yin abin da take bukata, wannan ba dama bace da zata doke ta ba, har ta yi mata rauni.
“Koda safe nan naga mahaifiyar ta Talata kafin naje na kai rahoto a ma’aikata, lokacin dana je can, ma’aikatar ta bada wasu jami’ai, wadanda suka raka ni, saboda a kama ta, amma kuma lokacin da muke je gidan, ta riga ta gudu da ‘ya’yanta,, na san ta sake fita ne, amma sais u jami’an suka bani tabbacin cewar za su kamata.”
Lokacin da aka tuntube shi wani jami’i na bunkasa harkokin yara, ma’aikatar mata da walwalar al’umma, Oluwaniyi Ogunley ya ce lalle an kama ita Bisola, da kuma yadda yarinyar tana samun sauk, a wata ganawar da aka yi da shi ta waya ranar Asabar.
Ogunleye ya ci gaba da bayanin, “ Mutane suna ta zuwa saboda su san irin halin da ake ciki dangane da shi al’amarin, don haka wannan ma sheda ce, wadda tke nuna yanzu mutane suna nuna damuwar su,musamman ma sanin irin halin da suke ciki a duk wuraren da muke. Mun yi kokari na samar da jami’an kulawa da kare yara, mun kuma je gidan , amma koda muka je matar da riga ta bar gidan ita da mijinta..
“ Da ya kasance bamu samu su iyayen ba da kuma yarinyar, sai muka samu mutanen da suke zaune kusa da su, suka kuma tabbatar mana da cewar, haka ne shi al’amarin ya auku,mun kuma dauki wasu matakai na samun wasu akan sa masu ido, duk lokacin da suka kasance,sai a kama su.
Ita gwamnatin jiha da gaske take na kare hakin yarana jihar, muna da amincewa da kuma goyon bayan gwamna. Ita kuma mahaifiyar yarinyar za’a gurfanar da ita gaban kotu, da zarar an kammala binciken da ake yi dangane da shi al’amarin.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!