Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Kama Mutum Biyu A Kan Kisan Dan Achaba A Ondo

Published

on

Sanadiyar mutuar animai sana’ar tuka mashin a Ipogun a cikin karamar Hukumar Ifedore ta jihar Ondo, ranar Alhamis, rundunar ‘yansanda ta jihar, ta bada bayanin kama mutane biyu, wadanda suke nasaba da abin da ya faru.
Shi dai mai mashin din wanda aka fi sani da Benjamin Falusi an dai samu rahoton an harbe shi ne, ya kuma mutu nan take lokacin da aka yi wani yamutsi lokacin da dan takarar kujerar majalisar wakilai ta tatarayya, a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party, Mista Tajudeen Adefisoye ya je wurin saboda ya yi kamfen.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda ta jihar Mista Femi Joseph, ya bayyana haka ne ranar Lahadi, ya kuma nunna cewar mutane biyu sune wadanda aka tarbatar da an kama su, wadanda suka hada da Bincent Akinde da kuma Olatunbosun Akinsanya, su an kama su saboda da aukuwar al’amrin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: