Connect with us

LABARAI

An Yi Gangamin Neman ‘Yancin Deji Adeyanju

Published

on

Gamaiyar kungiyoyi masu zaman kansu sun gudanar da zanga-zangar neman ‘yanci ga Deji Adeyanju wanda gwamnati take ci gaba da tsari shi, a wajen harabar gidan yarin jihar Kano. Masu zanga-zangar sun bayyana cewa, Adeyanju ya kwashe tsawan kwanaki 58 a tsare, bisa laifin da ake tuhumar sa da shi, duk da cewa babbar kotun jihar Kano ta wanke shi a shekarar 2009. Sun yi Allah wadai inda suka danganta lamarin da rashin adalci ga abokinsu, suna ta daga kwalaye wanda aka rubuta cewa suna kira a kan a sake shi nan take.
Jagororin kungiyoyin masu gudanar da wannan zanga-zanga sun hada da Ariyo-Ddare na kungiyar ‘Defence of Nigerian Democracy and Constitution’, Raphael Adebayo na kungiyar Free Nigeria Mobemen, Mosa Paul na kungiyar MADConnect da kuma Isaiah Umude na kungiyar Propel Africa Initiatibe.
Gamaiyar kungiyoyin sun bayyana rashin jin dadinsu game da halin da Adeyanju yake ciki, sun bayyana cewa mahaifiyarsa ta tsofa sannan tana cikin damuwa a kan halin da danta ke ciki.
Atoye ya bayyana cewa, Adeyanju shi ne shugaban kungiyar Concerned Nigerians, ba a damu da halin da yake ciki ba, inda ake ci gaba da tsare shi. Ya kara da cewa, ‘A ranar Lahadin nan ne muke gudanar da zanga-zangar kwanaki 58 da tsare dan uwanmu kwamoret Deji Adeyanju, a cikin wannan gwamnati na shugaban kasa Buhari a nan jihar Kano. ‘Ko da yake a yanzu haka yana tsare a cikin wani waje mai muni wanda kowa baya fatan zama a ciki, ina so wanda suke cikin fadar shugaban kasa su san da wannan lamari.’
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!