Connect with us

LABARAI

An Yi Kira Ga Matasa A Kan Su Rungumi Sana’o’i

Published

on

An yi kira ga matasa a jihar Kano su rika sana’oi na dogaro dakai ko harkokin kasuwanci da zasu rike kamsu dan hakan zai taimaka wajen yin anfani dasu ta hanyarda bata dace ba musamman gay an siyasa da suke angizasu domin tada husuma a lokacida ake zabe.Wani dankasuwa a kasuwar Dawanau Alhaji Mahadi Abdullahi ya yi wannan kiran.
Yayi nuni da cewa duba da karatowar kwanakin zabuka a kasar nan da yanda yanayi yake nunawa yakamata matasa su shiga taitayinsu ta kaucewa duk wani abu wanda bazai zama mai dadi ga al’umma ba,karsu yarda a yi anfani dasu wajen tada husuma a wajen zabe,su zama masu kare mutuncin kansu dana al’umma ta hanyar zuwa su zabi ra’a yinsu kuma kowama yaje ya zabi nasa hakan shine abinda yakamata.
Yayi nuni da cewa wabanda suke anfani da matasa a bangar siyasa su suna killace nasu ya,yan ta basu ilimi da aikinyi dan haka yakamat matasa masu bin yan siyasa su tsaya sy duba su gani akwai ya’yan wadanda ke sasu abinda bai dace a cikinsu su yiwa kansu fada su kaucewa yin abinda bazai anfani cigabansu ba.
Alhaji Mahadi ya kara da cewa ba wata kasa da za ta cigaba idan bata samu nagartattun matasa bad a suka san abinda yakamata dan haka idan matasa sunada sana’aryi hakan zai taimaka wajen kaucewa duk wani abu dazai jawo ayi anfani dasu ta hanyarda bata dace ba.
Ya kara da jan hankalin matasa da sauran al’umma su gujewa zagin shugabanni domin hakan bashida wata fa’ida saidai ya kara dulmiya al’umma cikin yanayi na rashin gyara amma idan ana yiwa shugabanni fatan alkhairi da kumayi musu addu’a dayi musu nasiha ta nuna musu abinda sukayi kuskure akai cikin mutuntawa hakan zaisa su zama nagari masu anfanarwa ga al’umma.
Ya kara da nuni da cewa abinda wasu suke a kafafen sadarwa na zamani na batanci da aibata shugabanni bai kamata ba,dan sai kaga anasa hoton sugabanni da mummunan shiga ta hada hotunansu wanda hakan ba abune mai kyauba yakamata duk abinda za’ayi ayishi ta hanyar mutuntaka.
Alhaji Mahadi Abdullahi yayi kira ga dukkan ilahirin al’ummar kasar nan da cewa zabukanda za’a shiga ayisu cikin lumana da zaman lafiya hakan shine zaisa a zabi shugabanni da suka dace kowa kuma zai zabi ra’ayinsa wanda nasa ra’ayin yakai ga nasara a hadu dan samarda cigaban kasar nan domin duk abinda zaman lafiya bai samar ba to rashinsa bazai samar dashi ba.Dan haka yakamata al’ummar kasar nan suyi koyi da sauran kasashe da suke zama abin misali a harkar zabuka a kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa da suke zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!